Assha: Mutane 3 sun mutu, 45 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake a Borno

Assha: Mutane 3 sun mutu, 45 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake a Borno

- Wasu hare haren kunar bakin wake guda biyu sun yi sanadiyyar mutuwar mutane ukku tare da jikkata wasu 45 a garin Muna Dalti da ke Maiduguri, jihar Borno

- Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, ta tabbatar da faruwar harin da aka kai a daren ranar Asabar

- Yan kunar bakin waken guda biyu wadanda dukkaninsu mata ne, sun tayar da bama baman da ke jikinsu bayan tazarar mintuna biyar tsakani a garin Muna Dalti

Wasu hare haren kunar bakin wake guda biyu sun yi sanadiyyar mutuwar wasu mambobin jami'an sa ai JTF guda biyu, farar hula guda daya tare da kuma jikkata wasu mutane 45 a garin Muna Dalti da ke Maiduguri, jihar Borno.

Shugaban tawagar kai agajin gaggawa na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno, Bello Dambatta, ya tabbatar da faruwar harin da aka kai a daren ranar Asabar.

A cewar Dabatta, mambobin jami'an sa kan sun hango 'yan kunar bakin waken dauke da abubuwan fashewa a jikinsu (PBIED), inda suka yi kokarin dakatar da su, amma suka tayar a bama baman da ya yi sanadin mutuwar 'yan kunar bakin waken tare da jami'an sa kan.

KARANTA WANNAN: Birnin-Gwari: Mutane da dama sun mutu a harin da yan ta'adda suka kai wajen biki

Assha: Mutane 3 sun mutu, 45 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake a Borno
Assha: Mutane 3 sun mutu, 45 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake a Borno
Source: UGC

Yan kunar bakin waken guda biyu wadanda dukkaninsu mata ne, sun tayar da bama baman da ke jikinsu bayan tazarar mintuna biyar tsakani a garin Muna Dalti.

Ya bayyana cewa wadanda suka jikkatan, sun samu raunuka da dama sakamakon fashewar bama baman, wadanda kuma ke kan samun kulawa daga likitoci a babban asibitin Maiduguri.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel