Buhari ya na farin ciki a kan samun nasarar kwato dukiyar kasa - Malami

Buhari ya na farin ciki a kan samun nasarar kwato dukiyar kasa - Malami

Ministan Shari'a kuma Lauya kolu na Najeriya, Abubakar Malami, ya fayyace daya daga cikin muhimman ababe na ci gaban kasa masu tasirin fidda ita zuwa tudun tsira da ke farantawa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari tare da Ministan Shari'a; Abubakar Malami

Buhari tare da Ministan Shari'a; Abubakar Malami
Source: Depositphotos

Ministan Shari'a kuma Lauyan kolu na Najeriya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi amanna tare da farin ciki kan samun nasarorin gwamnatin sa wajen dawo da dukiyar kasa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Malami ya fayyace hakan yayin bikin bayar da kyaututtuka na shekarar bara da aka gudanar a Ma'aikatar shari'a ta kasa da ke garin Abuja a ranar Lahadin da ta gabata kamar yadda kakakin sa, Salihu Othman Isah ya bayyana.

Malami ya ce ma'aikatar shari'a ta taka mataki na samun nasarori musamman a bangaren yaki da rashawa tare da wasu muhimman ababe na matse lalitar gwamnati gami da kwazon ta wajen rage cunkoso a gidajen yari.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun hallaka Mutane 8 a jihar Ribas

Ministan ya yi tozali da yadda gudanarwar ma'aikatar sa ta yi kwazon gaske wajen dawo da dukiyar kasa da gwamnatocin baya da yashe tare da jajircewa wajen shimfida ingatattun tsare-tsare masu hana duk wata almundahana.

Cikin na sa jawaban, sakataren dindindin na ma'aikatar shari'a Dapo Apata ya bayyana cewa, an gudanar da wannan taro na bayar da kyaututtuka domin yabawa kwazon aiki da kuma kara karsashi na jajircewa bisa aiku tukuru.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel