'Yan Bindiga sun hallaka Mutane 8 a jihar Ribas

'Yan Bindiga sun hallaka Mutane 8 a jihar Ribas

Kimanin rayukan Mutane takwas sun salwanta yayin da wasu 'yan kungiyoyin asiri masu adawa da juna su ka yi arangama a tsakanin su cikin yankin Rumuelumeni da ke karamar hukumar Obio Akpor ta jihar Ribas a ranar Lahadin da ta gabata.

Shugaban gundumar Rumuelumeni, Sunny Odum, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da wata kafar watsa labarai ta gidan radiyo a birnin Fatakwal. Ya ce tsama ta 'yan kungiyoyin asiri ta sanya suka fafata bakin gumurzu na harsashin bindiga.

'Yan Bindiga sun hallaka Mutane 8 a jihar Ribas
'Yan Bindiga sun hallaka Mutane 8 a jihar Ribas
Source: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Mista Odum ya ce arangamar harsashi na bindigu da ta auku da sanyin safiyar ranar Lahadi, ta salwantar da rayukan 'yan kungiyoyi asiri takwas nan take.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankali tare da ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum kamar yadda su ka saba yayin da hukumomin tsaro tuni sun tunkari lamarin wajen kwantar da tarzoma.

A yayin tuntubar kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Ribas, Nnamdi Omoni, cikin zayyana shaidar sa ya ce rayukan Mutane takwas ne kacal su ka salwanta yayin da Mutane uku suka jikkata a sanadiyar aukuwar mummunar ta'adar.

KARANTA KUMA: Fashewar Bam ta hallaka Mutane 5, 45 sun jikkata a Maiduguri

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar tsaro ta jami'an 'yan sanda, ta harbe wasu 'yan baranda uku murus maus ta'adar garkuwa da mutane a kauyen Kakanji na yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel