An fara siyasantar da kashe-kashen da ke aukuwa a Kaduna da Zamfara - Buhari

An fara siyasantar da kashe-kashen da ke aukuwa a Kaduna da Zamfara - Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce ba bu wani lamari mai muhimmanci da gwamnatin sa ke fafutikar tabbatarwa a halin yanzu face kawo karshen ta'addanci musamman yadda kashe-kashe da ta'adar garkuwa da mutane ta yi kamari a jihohin Kaduna da Zamfara.

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, shugaban kasa Buhari ya ce a halin yanzu ba bu wani shugaba a duniya da ya ke cikin kunci kamar sa duba da yadda ta'addancin masu garkuwa da mutane da kashe-kashe ya zamto ruwan dare a Kaduna da Zamfara.

A yayin da a ranar Asabar al'ummar Najeriya su ka gudanar da zanga-zanga na sukar halin ko in kula da gwamnatin Buhari ta ke yiwa lamarin ta'addanci a jihohin biyu na Arewa, shugaban kasa Buhari ya ce siyasa ta shiga cikin wannan lamari matukar za a yi masa irin wannan fahimta.

An fara siyasantar da kashe-kashen da ke aukuwa a Kaduna da Zamfara - Buhari

An fara siyasantar da kashe-kashen da ke aukuwa a Kaduna da Zamfara - Buhari
Source: Twitter

Cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, Buhari ba zai taba kasancewa cikin farin ciki matukar jinin al'ummar sa zai ci gaba da kwarara ba tare da hakki ba.

KARANTA KUMA: Zazzabin Lassa ya kashe Mutane 121 cikin watannin uku a Najeriya

Shugaban kasa Buhari cikin kausasa harshe ya ce siyasar kasar nan ta munana matukar 'yan adawa za su rika jifar sa da wannan mugun nufi na rashin damuwa yayin da ake yiwa talakawan sa kisan kiyash tare da kasancewar su cikin zaman dar-dar.

Yayin daura damara da tabbatar da tsayuwar daka wajen shimfida aminci na bayar da kariya ga al'ummar sa, shugaban kasa Buhari ya bayar da wa'adin awanni 24 ga dukkanin hukumomin tsaro da su gaggauta bincikar ta'adar da ke fuskantar jihohin Kaduna da Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel