Zazzabin Lassa ya kashe Mutane 121 cikin watannin uku a Najeriya

Zazzabin Lassa ya kashe Mutane 121 cikin watannin uku a Najeriya

Cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya, yayin bayar da tabbacin ci gaba da taduwar cutar zazzabin Lassa a kasar nan, ta ce rayukan Mutane 121 sun salwanta a Najeriya daga ranar 1 ga watan Janairun 2019 kawowa yanzu.

Cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya, ta tabbatar da salwantar rayukan Mutane biyu a jihohin Taraba da kuma Bauchi a sakamon kamuwa da cutar zazzabin Lassa.

Cikin wani sabon rahoto da fitar cibiyar ta tabbatar da yaduwar cutar cikin jihohin Edo, Ondo, Bauchi, Taraba da kuma Filato a tsakanin ranar 25 ga watan Maris zuwa ranar 31 ga watan.

Zazzabin Lassa ya kashe Mutane 121 cikin watannin uku a Najeriya

Zazzabin Lassa ya kashe Mutane 121 cikin watannin uku a Najeriya
Source: UGC

Ta ce kimanin Mutane 2,034 sun fara nuna alamu na kamuwa da cutar daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na shekarar 2019 cikin jihohi 21 da ke fadin Najeriya. Sai dai mutane 526 kacal aka tabbatar da kamuwar su da cutar.

KARANTA KUMA: An danne mana hakki a zaben gwamnan jihar Sakkwato - APC

A yayin da cutar zazzabin Lassa ta salwantar da rayukan Mutane 121 cikin watanni uku da suka gabata, jihohin da cutar ta yi kane-kane a halin yanzu sun hadar da Edo, Ondo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Plateau, Taraba, Adamawa, Gombe, Kaduna, Kwara, Benue, Rivers, Kogi, Enugu, Imo, Delta, Oyo, Kebbi, Cross River da kuma birnin Tarayya Abuja.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, cibiyar kula da yaduwar cututtuka ta Najeriya ta ce, kimanin ma'aikatan Lafiya 17 cikin jihohi 7 sun kamu da cutar zazzabin Lassa tun yayin barkewar ta karo na farko a Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel