Za mu dauki shekaru fiye da 10 gabanin gyara barnar da Boko Haram ta haifar a Najeriya - Buhari

Za mu dauki shekaru fiye da 10 gabanin gyara barnar da Boko Haram ta haifar a Najeriya - Buhari

A ranar Asabar din da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fayyace girman barnar da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta haifar a kasar nan ta Najeriya da gyaran ta ba zai yiwu cikin sauki ba.

Shugaban kasa Buhari kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ya ce za a dauki tsawon shekaru aru-aru a kasar nan gabanin gyara barnar da kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta haifar a kasar nan.

Buhari a kasar Jordan

Buhari a kasar Jordan
Source: Twitter

Buhari ya yi tozali da wannan furuci yayin gabatar da jawaban sa a taron tattalin arziki na duniya da aka gudanar a kasar Jordan inda ya fayyace girman barna da ta'addanci ya haifar wajen durkushewar Najeriya.

Cikin kalami na sa, shugaban kasa Buhari ya ce barna ta salwantar rayuka, asarar dukiya da kadara da kungiyoyin ta'adda irin su Al Qaeda, ISIS da kuma Boko Haram suka haifar, za a dauki tsawon fiye da shekaru goma gabanin farfadowa.

A yayin da Najeriya ke ci gaba da murna ta kasancewar ta mafi girman tattalin arziki a nahiyyar Afirka, shugaban kasa Buhari ya yi kira na neman shugabannin duniya a kan hada gwiwa da juna wajen inganta jin dadin rayuwar al'ummar su domin saukaka radadi na tashin-tashina da tarzoma.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya shilla zai halarci taro a kasar Rwanda

Shugaban kasa Buhari ya kuma bayyana farin cikin sa tare da godiya ga kasashen duniya da suka bayar da tallafi gami da gudunmuwa wajen yakar annobar ta'addanci da ya yi ma ta katutu musamman daular kasar Jordan karkashin jagorancin Mai Martaba Abdullahi II bin Al-Hussein.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, shugaban kasa Buhari bayan halartar taron tattalin arziki a kasar Jordan, ya kuma shilla Gabas ta Tsakiya domin halatar taron sanya hannu jari karo na 9 da za a gudanar a kasar Dubai a tsakanin ranar Litinin zuwa Laraba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel