Da duminsa: A yau shugaba Buhari zai isa Dubai domin halartar muhimmin taro

Da duminsa: A yau shugaba Buhari zai isa Dubai domin halartar muhimmin taro

- Shugaban kasa Buhari a yau (Lahadi) zai isa kasar Dubai, daular larabawa (UAE) domin halartar taron shekara shekara na saka hannun jari (AIM)

- Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya bar Abuja a ranar Alhamis, zai kuma dawo Nigeria bayan kammala taron saka hannun jari a Dubai

- Buhari zai gabatar da makala mai taken: "samun taswirar saka hannun jarin kasashen ketare kai tsaye: Bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar fasahar zamani"

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau (Lahadi) zai isa kasar Dubai, daular larabawa (UAE) domin halartar taron shekara shekara na saka hannun jari (AIM) da za a gudanar a karo na 9, wanda kuma za a fara a ranar Litinin.

Shugaban kasar zai garzaya Dubai daga babban birnin kasar Jordan, Amman, bayan halartar taron tattalin arziki na duniya (WEF) dangane da kasashen gabas da Arewacin Afrika da ya gudana a Dead Sea, Jordan.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Buhari ya bar Abuja a ranar Alhamis, zai kuma dawo Nigeria bayan kammala taron saka hannun jari a Dubai.

KARANTA WANNAN: Zaben gwamnan Bauchi: APC ta shigar da kara kotu, lauyoyi 50 za su kare PDP kyauta

Da ya samu gayyata ta musamman daga mai martaba, Sheikh Mohammed Bin Rashid Al Maktoum, mataimakin shugaban kasar daular larabawa, kuma firan minista, kuma sarkin Dubai, shugaban kasar Nigeria zai kasance bako na musamman da zai gabatar da jawabi kan makala mai taken, "samun taswirar saka hannun jarin kasashen ketare kai tsaye: Bunkasa tattalin arzikin duniya ta hanyar fasahar zamani."

A cewar masu shirya taron, taron zai kasance mai girma kasancewar zai tara manyan shuwagabannin duniya, masu zartaswa, 'yan kasuwa, masu saka hannun jari na gida da waje, kwararru kan saka jari da koyar da kasuwanci, da kuma kwararru kan fasahar sadarwa, tsare tsare da ilimi kan jawo FDI.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel