Zaben gwamnan Bauchi: APC ta shigar da kara kotu, lauyoyi 50 za su kare PDP kyauta

Zaben gwamnan Bauchi: APC ta shigar da kara kotu, lauyoyi 50 za su kare PDP kyauta

- Kungiyar lauyoyi ta BOBALAC ta ce a shirye ta ke ta tura lauyoyinta guda 50 domin kare zababben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed

- Kungiyar ta ce ta yanke wannan hukunci ne biyo bayan karar da gwamn Mohammed Abubakar ya shigar kotu kan kalubalantar zaben jihar

- Kungiyar ta ce karar da gwamnan ya shigar zai basu damar amfani da baiwar su wajen kare zabin al'umma wato zababben gwamnan jihar, Kauran Bauchi

Biyo bayan sanar da cewa gwamnan jihar Bauchi mai ci a yanzu, Mohammed Abdullahi Abubakar zai kalubalanci nasarar Sanata Bala Mohammed Abdulkadir a zaben gwamnan jihar da aka kammala a kotun sauraron korafe korafen zabe, wasu lauyoyi karkashin kungiyar BOBALAC sun ce a shirye suke su tura lauyoyinsu guda 50 domin kare zababben gwamnan, da kuma jam'iyyar PDP a kotun.

Kungiyar ta yi nuni da cewa wannan yunkuri da APC da gwamnan jihar Mohammed Abubakar suka yi na shigar da kara gaban kotu bayan shan kaye a zaben tamkar yin amai da lashewa ne, saboda tuni dai gwamnan ya amince da shan kaye da kuma taya zababben gwamnan Sanata Bala Abdulkadir Mohammed murna bayan sanar da sakamakon zaben a makon da ya gabata.

Kungiyar ta ce, "Bayan da ya amince da shan kaye da kuma taya Kauran Bauchi murnar lashe zabe, tare da sanin cewa wannan shi ne zabin al'umma, lallai da Mr Abubakar ya tsaya akan maganarsa ta farko, domin magana daya ita sarki ke kamawa,"

KARANTA WANNAN: Murabus: Buhari zai yanke hukunci kan makomar Onnoghen - Fadar shugaban kasa

Sanata Bala Mohammed

Sanata Bala Mohammed
Source: UGC

Mambobin kungiyar sun kara da cewa, a matsayinsu na lauyoyi, ba su da wata matsala da gwamna Mohammed Abubakar da jam'iyyar apc na zuwansu kotu domin kalubalantar nasarar Sanata Bala Abdulkadri Mohammed, kungiyar na mai cewa, "wannan ma yunkuri ne mai kyau domin hakan zai bamu damar yin amfani da baiwar da Allah ya bamu wajen kare zabin al'umma wato zababben gwamnan jihar, Kauran Bauchi".

Kungiyar BOBALAC ta karkare da cewa, "a kan hakan, muna tabbatarwa zababben gwamnan jihar da kuma daukacin al'umar jihar Bauchi cewa zamu tura akalla lauyoyinmu 50 da suka hada da manyan lauyoyi (SAN) domin kare zabin al'umma da kuma ganin mun samu nasara kan wannan kara da gwamna Abubakar ya shigar,"

Rahotanni sun bayyana cewa bayan da gwamnan jihar mai barin gado ya dawo jihar daga wata tafiya da yayi Abuja, Mohammed Abdullahi Abubakar ya shaidawa magoya bayan jam'iyyar APC cewa ya tuntubi shugaban kasa Muhammadu Buhari da shuwagabannin APC na kasa, inda suka yanke hukuncin garzayawa kotu domin kalubalantar nasarar Sanata Bala Mohammed Abdulkadir.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel