Murabus: Buhari zai yanke hukunci kan makomar Onnoghen - Fadar shugaban kasa

Murabus: Buhari zai yanke hukunci kan makomar Onnoghen - Fadar shugaban kasa

- Korarren alkalin alkalai na kasa, Walter Onnoghen bai yi murabus ba, ya rubuta takardar yin ritaya - Lauyan Onnoghen, Awomolo

- Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Muhammadu Buhari zai yanke hukunci kan makomar Onnoghen da zaran ya dawo daga kasar waje

- Jam'iyyar APC ta ce tana zargin akwai lauje cikin nadi kan labarin murabus din Onnoghen

Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yanke hukunci kan makomar korarren alkalin alkalai na kasa (CJN), Walter onnoghen da zaran ya dawo daga kasar waje a ziyarar taron kasashe da ya je UAE.

Wanan sanarwar ta fadar shugaban kasa ta zo ne jim kadan bayan da rahotanni suka bayyana cewa Onnoghen ya rubuta takardar murabus dinsa.

Da ya ke amsa tambayoyi daga jaridar Tribune domin bayar da tabbacin ko shugaba Buhari ya karbi takardar korarren alkalin alkalan, babban mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar watsa labarai, Garba Shehu, ya ce: "Iaya abunda zan iya fada maku a yanzu shi ne maganar Onnoghen na da matukar muhimmanci, Buhari zai yanke hukunci kan makomar Onnoghen da ya dawo kasar."

KARANTA WANNAN: Atiku ba shi da wata madafa kan kalubalantar nasarar Buhari - Junaid Mohammed

Murabus: Buhari zai yanke hukunci kan makomar Onnoghen - Fadar shugaban kasa
Murabus: Buhari zai yanke hukunci kan makomar Onnoghen - Fadar shugaban kasa
Source: UGC

Sai dai, babban lauyan Onnoghen, Chief Adegboyega Awomolo SAN, ya sanar da jaridar Tribune cewar Onnoghen ya rubuta wasikar yin ritaya ne ba wai wasikar murabus ya rubuta kamar yadda ake yadawa ba.

Ya ce: "Me zai sa ya yi murabus? Kawai dai ya rubuta takardar ritaya kamar yadda dokar kasar ta tanadar. Daga Janairu 15, ya ke cewa zai bi yadda doka ta tanadar, wacce ta baiwa NJC karfin ikon tuhumarsa, kuma ya ce zai bi duk hukuncin da majalisar ta tanadar, majalisar da ke da ikon hukuntga ma'aikatan fannin shari'a. Mu mun yarda da bin doka da oda ba kamar sauran ba.

"Tabbas, ya rubuta wasikar yin ritaya bayan da majalisar NJC ta yanke hukunci a ranar Alhamis."

Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Buhari ya tafi kasar Jordan da UAE. Ana sa ran zai dawo kasar bayan halartar taron shekara shekara kan sa hannun jari a Dubai, UAE da aka shirya gudanarwa daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Afrelu, 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel