PDP tayi amfani da Jami’an tsaro wajen murde zaben 2019 – Gwamna Ganduje

PDP tayi amfani da Jami’an tsaro wajen murde zaben 2019 – Gwamna Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yayi wata hira mai tsawo da Jaridar Daily Trust kamar yadda mu ka samu labari a Ranar Lahadin nan, 7 ga Watan Afrilu, inda ya tabo batutuwa da dama.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa shi ne wanda ya kirkiro jar hular da ‘Yan Kwankwasiyya su ke sanyawa a 2011, inda yace yanzu ya jefar da ita har abada. Gwamnan yace Mukarraban sa na da damar sa duk abin da su ke so.

Abdullahi Ganduje yace tarihin jar hula ya fara ne a lokacin yakin neman zaben 2011, wanda a lokacin Mai gidan sa Rabiu Kwankwaso da kuma Marigayi Ummaru Yar’adua su na neman takarar gwamna a jihar Kano da kuma shugaban kasa.

KU KARANTA: Muhimman abubuwan da ba ku sani ba a game da CP Wakili

Gwamnan yake cewa a wancan lokaci shi kuma yana cikin kwamitin yakin Dr. Goodluck Jonathan domin kuwa sun yi aiki tare a matsayin mataimakan gwamna a 1999. Ganduje yace a wancan lokaci ne ya kawo shawarar aiki da jar hula.

Dr. Ganduje yake cewa shi ne ya bada shawarar ‘Yan PDP a Kano su rika yin irin shigar Marigayi Malam Aminu Kano wanda aka sani da fararen kaya da jar hula da kuma bakaken takalma. Daga ranar kuma aka dauki wannan salo a Kano.

Haka kuma Gwamna Ganduje yayi magana a game da zaben jihar inda yace jam’iyyar PDP tayi amfani da jami’an tsaro, sannan kuma ta rika bada kudi wajen sayen kuri’u a cikin Birnin jihar Kano, wanda ya sa ya kusa rasa tazarce a zaben.

KU KARNTA: Sanatocin Kano za su goyi bayan Ahmad Lawan a Majalisa

Gwamnan jihar Kano din yake cewa babu shakka Kwamishinan ‘Yan Sanda Mohammed Wakili ya nuna son kai wajen aikin sa inda ya rika kama manyan APC da ke cikin gwamnati, ba tare da ya taba wani babban na jam’iyyar PDP a Kano ba.

Ganduje yace sam bai kamata CP Wakili ya taba mataimakin gwamna mai cikakken iko ba. Sannan kuma ya soki matakin da CP ya dauka na kyale tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso da mutanen sa na zuwa Garin Bebeji inda aka rasa rayuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel