Rikicin Majalisa: Sanatocin APC za su yi wa Jam’iyya taron dangi

Rikicin Majalisa: Sanatocin APC za su yi wa Jam’iyya taron dangi

Akwai alamun da ke nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta fuskanci irin barazanar da ta gamu da shi wajen zaben majalisar tarayya a 2015, inda ‘Ya ‘yan ta su ka hada-kai da jam’iyyar adawa ta PDP.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa akwai yiwuwar a sake samun irin wannan shiri da aka yi tsakanin Sanatocin jam’iyyar PDP da kuma na APC masu rinjaye a majalisa ganin inda jam’iyyar ta sake sa gaba a zaben majalisa da za ayi bana.

APC ta hakikance wajen ganin Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila sun samu shugabancin majalisar tarayyan. Sai dai kuma wasu ‘Yan majalisa na jam’iyyar sun nuna rashin amincewar su game da wannan mataki da aka dauka.

KU KARANTA: Buhari zai yi bayani a gaban manyan Duniya a kasar UAE

Duk da jam’iyyar APC ta tsaida Ahmad Lawan, akwai ‘Ya ‘yan ta irin su Mohammed Ali Ndume da kuma watakila Mohammed Danjuma Goje da ke neman wannan kujera ido-rufe. Ana tunanin Sanata Abdullahi Adamu ya janye takara.

Danjuma Goje yayi gum da bakin sa, amma rahotanni sun nuna cewa har gobe yana harin kujerar shugaban majalisar dattawan. Tsohon gwamnan na Gombe yana cikin Sanatocin Arewa ta Gabas da su ka dade a majalisar tarayya.

Shi kuwa Sanata Mohammed Ali Ndume a na sa bangaren, bai boye shirin sa ba, inda ya fito ya bayyana cewa ya sha alwashin yin takara da Ahmad Lawan. APC tana da Sanatoci 65 ne yayin da PDP kuma ta ke da 43 a majalisa ta 9 mai zuwa.

KU KARANTA: 2019: Jam'iyyar APC ta samu kujeru 65 a Majalisar Dattawa ta 9

Ahmad Lawan dai yana ta kokarin ganin yadda zai shawo kan Sanatocin jam’iyyar sa ta APC, wannan ya sa ya zauna da wasu gwamnonin APC kwanan nan. Sai dai da alama yadda APC ta zakulo Lawan din bai yi wa Sanatocin ta dadi ba.

‘Yan APC sun so ace an bi tsari na lalama wajen fitar da wanda ake so ya gaji Saraki, amma hakan bai yiwu ba. Sanatocin APC masu neman wannan kujera za su iya shiga yarjejeniya da PDP domin su kai ga ci kamar yadda aka yi a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel