Sanata Adeleke ya cancanci ya rike Gwamnan Osun inji Kotu

Sanata Adeleke ya cancanci ya rike Gwamnan Osun inji Kotu

Kotun daukaka kara da ke zama a cikin Garin Akure a jihar Ondo ta tabbatar da cancantar tsayawa takarar gwamnan jihar Osun da Sanata Ademola Adeleke yayi har kuma ake ikirarin ya lashe zabe.

A jiya Asabar 6 ga Watan Afrilu ne babban kotun ta rusa hukuncin da wani Alkalin kotun tarayya yayi a Abuja, wanda ya zartar da cewa Ademola Adeleke bai cika sharudan da ake nema wajen tsayawa takarar kujerar Gwamna a Najeriya ba.

Alkali M. A Danjuma yayi watsi da wannan hukunci na kotun tarayya na Bwari inda ya amince da rokon ‘dan takarar gwamnan, ya kuma soke matakin da karamar kotun ta dauka a makon da ya gabata a kan wasu manyan dalilai har uku.

KU KARANTA: Hikimar da ta sa Onnoghen ya mikawa Buhari takardar ajiye aiki

Sanata Adeleke ya cancanci ya rike Gwamnan Osun inji Kotu
Ana zargin cewa Ademola Adeleke bai rubuta jarrabawar WAEC ba
Asali: Depositphotos

Daga cikin dalilan da Alkalin kotun daukaka karar ya bada shi ne tun farko kotun tarayyar ba ta da hurumin sauraron wannan kara a kan Ademola Adeleke da wani Kingsley Awosiyan ya kawo mata har ta kai a rusa takarar Sanatan.

Sauran Alkalan da su ka bada wannan hukunci a zaman da aka yi su ne Alkali mai shari’a R.A Abdullahi da kuma P.A Mahmoud. Alkalan sun ce sam kotun da ke zama a Bwari bai kamata ta sabawa hukuncin da ‘yar uwar ta tayi a da ba.

A Satumban bara wasu manyan kotu sun tabbatar da cewa Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya cika duk matakan da ake bukata na tsayawa takarar gwamna. Daga baya ne wani kotu da ke Abuja ya ruguza wannan shari’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel