Yadda uwar-bari ta sa babban Alkalin Najeriya yayi murabus kafin lokacin sa

Yadda uwar-bari ta sa babban Alkalin Najeriya yayi murabus kafin lokacin sa

Babu mamaki matsin lambar daga fadar shugaban kasa da kuma binciken da majalisar shari’a ta Najeriya watau NJC ta bada game da Walter Onnoghen yana cikin abin da ya sa ya rubuta takardar murabus.

Daily Trust, a rahoton da ta fitar a Ranar Asabar, 6 ga Watan Afrilun 2019, ta bayyana cewa hurowa Mai shari’a Walter Onnoghen wuta da aka yi ko ta ina, bai rasa nasaba da ajiye aikin da yayi a karshen makon jiyan da ya gabata.

Ko da dai fadar shugaban kasa ba tace komai har yanzu game da ajiye aikin da Alkalin Alkalan Najeriya yayi ba, amma alamu sun nuna cewa ya nemawa kan sa sauki ne bayan samun labarin sakamakon binciken da aka yi a kan sa.

A ka’ida babban Alkali mai shari’a Walter Onnoghen zai yi ritaya ne a karshen 2020, amma dole ta sa ya nemi ya bar aikin na sa bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shi kwanaki bisa wasu zargi na sabawa ka’idar aiki.

KU KARANTA: Shugaban Najeriya Buhari ya zauna da Sarkin Kasar Jordan

Yadda uwar-bari ta sa babban Alkalin Najeriya yayi murabus kafin lokacin sa

Dole ta sa JN Walter Onnoghen ya ajiye aikin sa a Kotun koli
Source: UGC

Majiyar jaridar tace babban Alkalin na Najeriya ya rubuta takardar murabus ne domin ya samu damar karbar kudin sallamar sa da aka ware masa. Wannan kuma zai sa ya gujewa binciken kwa-kwaf daga wajen hukumomin kasar.

Tun kafin yau dai majalisar NJC ta kasar ta so ace Walter Onnoghen ya ajiye aikin na sa salin-alin domin gudun a batawa bangaren shari’a suna. A yanzu dai wannan mataki da Alkalin kotun kolin ya dauka ya zama masa dole.

Fadar shugaban kasa ta bakin Garba Shehu ba tayi magana game da batun ba, amma rahotanni sun nuna cewa shugaban kasa ba zai ji dadin binciken da NJC tayi ba domin babu wani laifin Alkalin da aka zayyano a rahoton da aka fitar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Online view pixel