Kudu ta manta da kujerar shugaban kasa - Junaid Mohammed

Kudu ta manta da kujerar shugaban kasa - Junaid Mohammed

Junaid Mohammed, mamba a majalisar wakilai a jamhuriya ta biyu, ya ce kudancin Najeria ya manta da samun kujerar shugaban kasa a shekarar 2023 matukar arewa zata tsayar da dan takara a zaben shekarar.

Tsohon dan majalisar ya yi ikirarin cewar tsarin mulkin karba-karba a tsakanin yankunan Najeriya ya lalace, a saboda haka duk yankin da yake da yawan jama'a shine zai samar da shugaban kasa, ya zargi 'yan kabilar Igbo da karbar miliyoyi domin goyon bayan Atiku.

Yayin wata hira da ya yi da jaridar Leader NG, Junaid ya ce an hada baki da mutanen da ya kamata su kare doka wajen tafka murde zaben shekarar 2019.

Da aka tambaye shi a kan tsarin karba-karba domin tabbatar da adalci, Junaid ya ce; "bana son jin maganar wani adalci, don duk zancen banza ne. Mutanen kudu, musamman na yankin 'yan kabilar Igbo, ne suka fara lalata tsarin karba-karba ta hanyar kin bayar da kuri'unsu ga duk dan takarar da aka tsayar domin tabbatar da tsarin.

Kudu ta manta da kujerar shugaban kasa - Junaid Muhammed

Junaid Mohammed
Source: Facebook

"Zasu iya cewa lokacin mu ne, amma ba zamu zabe su b, sai mu ga abinda zai faru. Ka duba yadda 'yan kabilar Igbo suka zazzaga kuri'unsu ga Atiku a zaben da ya wuce, kuma a haka suke so ragowar jama'ar dake sassan kasar nan su zabi dan takaraR su a nan gaba. Idan kuna son ragowar 'yan Najeriya su zabe ku, dole ku bayar da hadin kai wajen zaben nasu dan takarar.

"Watakila Nnamdi Kanu suke so ya tilasta wa 'yan Najeriya su zabi dan takarar su. Ita siyasa 'yar musaya ce; ka bani, na baka, kamar yadda Michael Opara ya saba fadi.

DUBA WANNAN: Kisan kare dangi: 'Yan Zamfara sun gudanar da zanga-zanga a Abuja

"Ban san ta yaya suke tsammanin jama'a zasu zabe su ba, ni dai ba zan basu kuri'a ta ba. Basu zabi dan takarar da suke son jama'arsa su zabe su ba, sannan bayan hakan sun shiga jaridu suna zagin mutane. Bari mu gani idan hakan ne zai basu kuri'u lokacin zabe."

Junaid ya kara da cewa jama'ar yankin kudu maso gabas, na 'yan kabilar Igbo, sun ki koyar darasi daga irin kura-kuran da suka yi a baya.

Sannan ya cigaba da cewa; "dubi yadda tun yanzu aka fara cece-kuce a kan takarar shugaban kasa a 2023, kabilar Yoruba na cewa ma juyinsu ne su fito da dan takarar shugaban kasa; ko da wacce hujja suka dogara wajen ayyana hakan?"

Daga karshe, Junaid ya bayyana cewar lashe zabe ya dogara ne da yawan kuri'a tare da bayyana cewar yankin da ya fi yawan jama'a ne zai cigaba da samun damar lashe zaben kujerar shugaban kasa tunda kowa nasa yake zaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel