Kisan kare dangi: 'Yan Zamfara sun gudanar da zanga-zanga a Abuja

Kisan kare dangi: 'Yan Zamfara sun gudanar da zanga-zanga a Abuja

'Yan asalin jihar Zamfara dake zaune a Abuja sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukan matakin da zai kawo karshen kashe-kashe da sace mutane dake faruwa kullum ta Allah a jihar.

Da suke gudanar da zanga-zangar ranar Asabar, 'yan asalin jihar ta Zamfara sun bayyana rashin jin dadinsu a kan rashin zaman lafiyar da ya raba jama'a da gidajensu ya kuma saka jama'ar jihar zama cikin kunci baya ga asarar rayuka da dukiya.

A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa, Fatimah Mustapha, wacce ta shirya zanga-zangar, ta ce sun yi hakan ne domin jan hankalin gwamnatin tarayya a kan yadda ake yiwa jama'ar Zamafara kisan kare dangi tare da yin garkuwa da su.

A cewar ta, rashin daukan kwakwaran mataki a bangaren gwamnati na kara wa 'yan ta'addar jihar karfi da kwaron gwuiwa.

Kisan kare dangi: 'Yan Zamfara sun gudanar da zanga-zanga a Abuja

'Yan Zamfara sun gudanar da zanga-zanga a Abuja
Source: Twitter

Ta ce gwamnatin jihar Zamfara bata yin komai wajen ganin ta shawo kan lamarin, ta kara da cewa hakan yasa suka yanke shawarar gudanar da zanga-zanga a Abuja.

Gogaggiyar 'yar jarida, Kadaria Ahmed, na daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar, tayi kira ga shugaba Buhari da ya bawa jami'an tsaro umarnin kawo karshen aiyukan ta'addanci a jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Artabu: Dillalan kwaya sun kone ofishin jami'an NDLEA a jihar Jigawa

"Akwai kalubalen tsaro a fadin Najeriya, amma abinda ke faruwa a jihar Zamfara ya yi munin gaske. Mun gaji da binne mutane a kowacce rana kuma saboda haka ne muke kira ga shugaba Buhari da ya yi wani abu a kan lamarin," a cewar ta.

Wani tsohon hadimin gwamna Yari, Zaharudden Bello-Imam, ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki tsatsauran mataki a kan masu sace mutane da 'yan biniga a jihar Zamfara.

NAN ta rawaito cewar masu zanga-zangar sun fara ne daga 'Unity Fountain', inda suka fara tattaki har zuwa fadar shugaban kasa tare da mika wata wasika ga shugaba Buhari.

Da yake magana da masu zanga-zangar, Usman Ibrahim, mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren tsaro, ya ce zai mika sakonsu zuwa ga shugaban kasa. (NAN).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel