Atiku ba shi da wata madafa kan kalubalantar nasarar Buhari - Junaid Mohammed

Atiku ba shi da wata madafa kan kalubalantar nasarar Buhari - Junaid Mohammed

- Junaid Mohammed, ya ce tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya kitsa tuggun yadda ake tafka magudin zabe tun daga shekarar 1999

- Da wannan Junaid ya ce Atiku na rura wutar siyasar kasar ta hanyar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Fabreru

- Mohammeed ya kuma yaba kan irin ci gaban da aka samu a bangaren zabe, inda yanzu kowanne dan Nigeria zai iya yin zabe a kowanne gari yake zaune

Junaid Mohammed, dan majalisa a mulkin farar hula na biyu, ya ce tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya kitsa tuggun yadda ake tafka magudin zabe tun daga shekarar 1999, don haka ba shi da wata makama akan cewa an tafka magudi a zaben 2019.

Ya kuma zargi Atiku, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP na rura wutar siyasar kasar ta hanyar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabreru, wanda ya baiwa shugaba Muhammadu Buhari damar komawa mulki a karo na biyu.

Da ya ke zantawa da jaridar The Sun, Mohammeed ya kuma yaba kan irin gagarumin ci gaban da aka samu a bangaren gudanar da zabe, inda yanzu kowanne dan Nigeria zai iya yin zabe a kowanne gari yake zaune.

KARANTA WANNAN: Zamafara: Jami'an sa kai na CJTF sun yi fito na fito da 'yan ta'adda, an kashe mutane 50

Junaid Mohammed

Junaid Mohammed
Source: Depositphotos

Da ya ke amsa tambayoyi akan wannan mataki da Atiku ya dauka na kalubalantar sakamakon zaben, ya ce: "Bani da masaniya ko Atiku ya yi hakan domin rura wutar siyasar kasar, amma maganar dai guda daya ce, sam bai kyautu ya kalubalanci sakamakon zaben ba.

"Kowanne dan Nigeria kuma mai kishi ya san cewa idan aka rura wutar siyasa kamar yadda aka rura ta yanzu, a karshe rikici ne ke barkewa; za a samu jerin gwanon jama'a da za su tilasta kansu yin hijira saboda rikicin da zai iya barkewa.

"Babban dalilin da ya sa Atiku ya shigar da kara ba zai wuce sanin cewa ya fadi zabe ba; walau shi ya fada ko wadanda ke tare da shi ne suka fada. Sanarwar da Secondus ko jama'arsu ke fitarwa a yanzu ta koma ta zargi da cin mutunci ba wai ga 'yan APC ba hatta ga wadanda suka sa hannu a zaben. Ni a nawa ganin wannan rashin da'a ne, ba sai na zage ka ba ne sannan ka zabe ni.

"Ai ba zamu manta yadda Atiku ya kitsa tuggun murde zaben 1999 ba, lokacin da Obasanjo da shi suka samu tikitin takara. Idan har ka yi irin hakan, bai kamata ka yi mamaki don mutane sun yi abunda kai ka koyar da su ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel