Kabilar Igbo sun yi murna da nasarar Bala Mohammed a Bauchi

Kabilar Igbo sun yi murna da nasarar Bala Mohammed a Bauchi

Wata kungiyar kabilar Igbo sun nuna farin cikin su akan samun nasarar zababben gwamnan jihar Bala Muhammed Kaura da kuma jam'iyyar PDP

Kungiyar Kabilar Igbo da ke jihar Bauchi sun taya zababben gwamnan jihar Sanata Bala Abdulkadir Mohammed Kaura murna, inda suka yi alkawarin ba da goyon bayansu dari bisa dari ga gwamnan da kuma jam'iyyar (PDP).

Kungiyar ta fitar da wannan sanarwar ne, a wata takarda wacce shugaban kungiyar Injiniya Dominic Nkwocha (JP), da kuma Sakataren kungiyar Patrick Felix Onuorah (JP) su ka fitar.

Kabilar Igbo sun yi murna da nasarar Bala Mohammed a Bauchi

Kabilar Igbo sun yi murna da nasarar Bala Mohammed a Bauchi
Source: UGC

Ya ce, "Ya kamata a sani cewa kabilar Igbo dake jihar Bauchi sun fito kwansu da kwarkwatarsu sun zabi jam'iyyar PDP, kuma za a tabbatar da hakan a kowacce rumfar zabe," in ji Nkwocha.

Har ila yau kabilar Igbo ta nesanta kanta da rahoton da aka fitar a ranar 6 da 7 ga watan Maris, 2019 da ke nuna cewar kabilar Igbon sun sanar da cewar basa goyon bayan jam'iyyar PDP.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

Ba mu da masaniya akan wannan rahoto, "Sannan muna so mu sanar da cewa kwamitin da ta rubuta wannan rahoton ta yi ne ba da hannun kungiyar kabilar Igbo ba.

"Game da bayanin da aka ambata a sama, muna nesanta kungiyar kabilar Igbo daga wannan bayani saboda bashi da tushe, kuma koda ma anyi ba da sa hannun jagororin kungiyar mu bane."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel