Babu wata doka da take nu na cewar Osinbajo ne zai gaji shugaba Buhari a 2023 - Babachir Lawal

Babu wata doka da take nu na cewar Osinbajo ne zai gaji shugaba Buhari a 2023 - Babachir Lawal

- Babachir ya ce jam'iyyar APC ba ta ce za ta bawa Osinbajo kujerar shugaban kasa ba

- Sannan ya ce dan arewa ya na da damar da zai fito neman takara, tun da babu wata doka da ta hana yin hakan

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya fadawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kada ya yi tsammanin za a zabe shi a matsayin wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zabe a karo na biyu, akan yarjejeniyar cewar 'yan yankin kudu za su bawa shugaban kasar dama a karo na biyu, sannan idan wani zagayen ya dawo za a bawa yankin kudu kujerar shugaban kasar.

Ba wata doka da ta ce Osinbajo ya gaji shugaba Buhari a 2023 - Babachir

Ba wata doka da ta ce Osinbajo ya gaji shugaba Buhari a 2023 - Babachir
Source: UGC

Shugabannin jam'iyyar APC, Osita Okechukwu da Joe Igbokwe, suna daga cikin wadanda suka bayyana cewa yankin kudu maso gabas za a bawa kujerar shugaban kasar, yayinda Mista Osinbajo da Babatunde Fashola suka bukaci a bawa yankin kudu maso yamma.

Amma Mista Lawan, tsohon na hannun daman shugaba Buhari ya ce, jam'iyyar APC ba ta yi wa mataimakin shugaban kasa Osinbajo alkawarin kujerar takara ba, sannan kuma babu wata doka da ta bayyana cewa mataimakin shugaban kasa ne zai gaji shugaba Buhari idan ya sauka daga mulki.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

Babachir ya ce shi ba wai yana jayayya da 'yan kudu ba ne akan kujerar shugaban kasar, amma kuma hakan ba wai yana nufin duk wani dan arewa da ya ke da sha'awar fitowa takara kin fitowa ba.

Babachir Lawal, ya yi Sakataren Gwamnatin Tarayya, daga shekarar 2015 zuwa watan Oktoba na shekarar 2017, lokacin da aka koreshi daga aiki bayan an kama shi da laifin cin hanci da rashawa da wasu kudade da aka bai wa wadanda rikicin Boko Haram ya rutsa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel