Yanzu-yanzu: An tsinci gawar wani kone kurmus cikin motarsa a Bauchi

Yanzu-yanzu: An tsinci gawar wani kone kurmus cikin motarsa a Bauchi

An tsinci gawar wani mutum mai suna Ibrahim Hameed Majim a kone kurmus a cikin motarsa a jihar Bauchi.

Daily Trust ta ruwaito cewa an gano gawarsa da motar a cikin daji a unguwar Rogo da ke karamar hukumar Toro na jihar Bauchi.

An zaton mutumin ne ya kashe kansa saboda wasu mazauna garin sunyi ikirarin cewa ya na nuna alamun damuwa idan har suka ce ya taba fadin cewa ya gaji da rayuwa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa kafin rasuwarsa mutumin yana aiki ne da Kwallejin Fasaha na Tarayya na jihar Bauchi.

DUBA WANNAN: Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Yanzu-yanzu: An tsinci gawar wani mutum a kone kurmus cikin motarsa a Bauchi

Yanzu-yanzu: An tsinci gawar wani mutum a kone kurmus cikin motarsa a Bauchi
Source: Twitter

A hirar da akayi da shi a wayar tarho, Mai magana da yawun makarantar, Malam Rabiu Wada ya tabbatar da cewa mammacin ma'aikacin makarantar ne.

"Eh, ma'aikacin mu ne. Cikin 'yan kwanakin nan ya nemi a bashi hutunsa na wata guda inda ya ce zai tafi Kaduna kuma daga baya muka samu labarin a tsinci gawarsa a cikin motarsa da aka kona.

"Ofishin 'yan sanda na Toro ne suka kira ne suka sanar da ni abinda ya faru. Sun aiko min wasu hotuna saboda in tabbatar musu idan shine kuma na gane cewa shi ne," inji shi.

Ya kuma musanta jita-jitan da wasu ke yadawa na cewa rashin bawa ma'aikacin gurbin karo karatu a kasar waje ne ya sanya shi ya shiga damuwa har ya kashe kansa.

"Wannan ba gaskiya bane. Asusun Tetfund ne ke bayar da gurbin karo karatu ga malaman Jami'a kuma shi ba malami bane."

Kakakin 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce har yanzu ana gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel