Yari ya gaza mana – Masu zanga-zanga sun mamaye Aso Rock kan kashe-kashen Zamfara

Yari ya gaza mana – Masu zanga-zanga sun mamaye Aso Rock kan kashe-kashen Zamfara

Wasu masu zanga-zanga sun yi tattaki zuwa fadar Shugaban kasa da ke Abuja a ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu kan kashe-kashen jihar Zamfara.

Hakan ya biyo bayan kisan kiyashin da wasu da ake zargin yan fashi ne suka yiwa mutane a jihar.

A ranar Juma’a, 5 ga watan Afrilu ne, Sansi Rikiji, kakakin majalisar dokokin jihar, ya kai ziyarar jaje zuwa masarautar Kaura Namoda inda aka kashe yan tsaron sa kai na CJTF akalla su 50 cikin kwana daya.

Duk da tura dubban jami’an tsaro da aka yi bisa umurnin Shugaban kasa Muhamadu Buhari a watan Yulin 2018, lamarin tsaro bai inganta ba.

Yari ya gaza mana – Masu zanga-zanga sun mamaye Aso Rock kan kashe-kashen Zamfara

Yari ya gaza mana – Masu zanga-zanga sun mamaye Aso Rock kan kashe-kashen Zamfara
Source: UGC

Abdulaziz Yari, gwamnan jihar Zamfara, ya sha caccaka akan rashin yin kokari sosai don kakkabe ayyukan yan ta’addan.

KU KARANTA KUMA: Masu garkuwa sun saki ma'aikacin gwamnatin da aka sace a yammacin ranar auren yarsa

Akwai lokacin da Yari yayi murabus daga matsayin Shugaban tsaro na jihar.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, masu garkuwa da mutane sun saki kakakin hukumar NiMET, Mista Muntari Yusuf, wanda aka yi garkuwa dashi ranar Talata a hanyar babban titin Kaduna zuwa Abuja.

An tattaro cewa wadanda suka yi garkuwa dashi sun sake shi ne a yammacin ranar Juma’a wanda yayi fdaidai da yammacin auren yarsa.

Kakaki NiMET din wanda yayi nasarar tsira a wani mumunan hatsarin mota da rauni da dama, ya kuma yi nasarar bayar da auren yarsa, Hassana Mukhtar Yusuf ga Saifullah Abdulaziz a yau Asabar, 6 ga watan Afrilu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel