Masu garkuwa sun saki ma'aikacin gwamnatin da aka sace a yammacin ranar auren yarsa

Masu garkuwa sun saki ma'aikacin gwamnatin da aka sace a yammacin ranar auren yarsa

Masu garkuwa da mutane sun saki kakakin hukumar NiMET, Mista Muntari Yusuf, wanda aka yi garkuwa dashi ranar Talata a hanyar babban titin Kaduna zuwa Abuja.

An tattaro cewa wadanda suka yi garkuwa dashi sun sake shi ne a yammacin ranar Juma’a wanda yayi fdaidai da yammacin auren yarsa.

Kakaki NiMET din wanda yayi nasarar tsira a wani mumunan hatsarin mota da rauni da dama, ya kuma yi nasarar bayar da auren yarsa, Hassana Mukhtar Yusuf ga Saifullah Abdulaziz a yau Asabar, 6 ga watan Afrilu.

An tattaro cewa iyalansa da masu fatan alkhairi ga babban jami’in na NiMET, sun yi nasarar tattara kudin biyan masu garkuwan, kwanaki hudu bayan sun yi garkuwa da su.

Masu garkuwa sun saki kakakin NIMET a yammacin ranar auren yarsa

Masu garkuwa sun saki kakakin NIMET a yammacin ranar auren yarsa
Source: Facebook

Kan yadda aka sace Mista Yusuf, wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwan sun zo da moto i biyu inda na farkon ya toshe gaban motar kakakin NiMeET din, kirar Peugeot 408, yayinda dayan ya tare su ta baya.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai zarce Kasar UAE idan an gama taro a Jordan

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Muntari Yusuf, wani ma’aikacin gwamnati da aka sace a hanyar Abuja zuwa Kaduna ya umurci iyalansa da su siyar da motarsa sannan su cire naira miliyan biyu da ya sauran masa a asusun bankinsa domin biyan kudin fansar da masu garkuwa dashi suka bukata.

A wani hiran waya da aka nada na Mallam Yusuf, da dan’uwansa Nura, da kuma daya daga cikin wadanda suka sace shi, da fari dai masu garkuwan sun bukaci naira miliyan 50.

A lokacin da iyalansa suka tara naira miliyan shida, sai masu karkuwan suka ki amincewa da hakan, inda suka bayyana lamarin a matsayin aikin banza.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel