Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Wani mutum mai shekaru 40 a dan asalin kasar Iraqi ya halaka budurwarsa a kasar Austria saboda ta masa gori a kan kankantar mazakutarsa.

A cewar jaridar Mirror UK, mutumin mai suna Daban K dan asalin kasar Iraqi ya kashe budurwarsa wadda ta bashi mafaka na tsawon shekaru domin kaucewa arangama da jami'an tsaro na kasar Austria.

Matar ta bawa Daban masauki ne a gidan ta bayan ya ki amincewa ya koma kasarsa ta Iraqi kamar yadda mahukunta Austria suka bukata.

DUBA WANNAN: Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa

Saurayi ya kashe wacce zai aura saboda ta raina girman mazakutarsa
Source: Twitter

Bayan jami'an tsaro sun kama shi inda ake tuhumarsa da laifin kisan kai, Daban ya ce ya daba wa sahibarsa wuka ne a wuyanta a kalla sau hudu saboda gori da izgili da ta ke masa kan kankantar mazakutarsa da kuma bin wasu mazaje.

A hirar da Daban K ya yi da likitan kwakwalwa, Sigrun Rossmanith ya ce, "Ta kyautata min sosai amma kuma ta ci mutunci ne sau da yawa.

"Ta ci amana ta da maza uku kuma daga baya tana kaurace min a shimfidar mu. Wata rana sai ta bude baki ta ce min mazakuta ta tayi mata kankanta sosai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel