Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

Ana sa ran kafin shugaba Muhammdu Buhari ya fara gabatar da mulkin sa zai yi tankade da rairaya akan 'yan majalisar fadar ta sa musamman ma ministocinsa

A ranar 29 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fara gabatar da mulkinshi karo na biyu, wanda kuma shine mulkinshi na karshe kamar yadda dokar kasa ta nuna.

Kafin karshen wannan mulkin na shi ana tunanin shugaban kasar zai yi tankade da rairaya akan 'yan majalisar fadarsa da kuma ministocin sa. An jima ana ba wa shugaban kasar shawara akan ya canja wasu daga cikin ministocin na sa, musamman wadanda ba su tabuka komai ba.

Duk da rashin kokarin wasu daga cikin ministocin na shi, amma shugaban kasar haka ya yi hakuri ya cigaba da tafiya da su, amma da yawa daga cikinsu sunyi abin a zo a gani, wanda suka cancanci shugaban kasar ya tafi dasu a karo na biyu.

Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su

Jerin Ministocin da shugaba Buhari zai koma mulki da su
Source: UGC

Wasu daga cikin ministocin da ake sa ran shugaban kasar zai tafi da su sun hada:

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed

Duk da cewa ya na da kusanci da jigon jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, amma ya yi kokari mutuka wurin ganin shugaba Buhari ya lashe zaben jihar Kwara.

Ministan Noma, Cif Audu Ogbe

Cif Audu Ogbe na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, tun lokacin da jam'iyyar PDP ta cire shi a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Shugaba Buhari ya yaba mishi da irin kokarin da ya yi ta fannin kawo cigaba a harkar noma a kasar nan, sannan kuma ya kokari wurin rage shigo da shinkafa daga kasashen waje zuwa kasar nan.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya na daya daga cikin ministocin da ake sa ran shugaba Buharizai cigaba da mulki da shi. Ministan wanda ya ke dan asalin jihar Bauchi ya na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, tun lokacin da shugaban kasar ya ke ciyaman din man fetur. Alamu na nuna cewa shugaban kasar beyi watsi da manyan abokansa ba.

Ministan Kimiyya da Fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu

Dr. Onu shine ministan kimiyya da fasaha a yanzu, sai dai ba kowane ya san shi ba a kasar nan, amma duk da haka akwai yiwuwar shugaba Buhari zai cigaba da mulki da shi, amma kuma ganin irin dangantakar da ke tsakanin shugaban kasar da gwamnan jihar Ebonyi, Injiniya Dave Umahi, akwai yiwuwar ministan ya rasa kujerar shi. Saboda jihar Ebonyi ita ce jihar da tafi bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari kuri'u a yankin kudu maso gabas.

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola

Tsohon gwamnan jihar Legas din, shine ministan aiyuka da gidaje a yanzu. Ya na daya daga cikin jiga-jigan gwamnatin Buhari, hatta Buhari ya na yaba irin aikin da ya ke yi, saboda haka ne ma shugaban kasar ya bashi mukamai uku a lokaci daya. Duk da cewa dai akwai maganganu da ke nuna cewar ministan bai yi wani kokari a bangaren wutar lantarki ba.

Bayan haka kuma, ganin yadda gwamnan Legas na yanzu bai samu koma mulki ba, akwai yiwuwar shugaban kasar zai karbi bangare daya daga cikin aiyukan da ya bawa Fasholan don ya bawa Ambode, saboda yana daya daga cikin gwamnonin da suka fi kokari a kasar.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi

Amaechi shine Ministan Sufuri, sannan kuma darakta janar na kamfen din shugaba Buhari. Tsohon gwamnan jihar Rivers din ya na daya daga cikin ginshikan jam'iyyar APC a yankin kudu. Sannan ya yi bakin kokarin sa a lokacin zaben fidda gwani da aka yi na shugaban kasa a shekarar 2014.

KU KARANTA: Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika

Hadi Sirika shine Ministan sufurin jiragen sama. Ya samu yabo da yawa na irin aikin da ya ke yi a fannin jiragen sama. Sai dai kuma akwai yiwuwar Sanata Abu Ibrahim zai iya karbar kujerar ta shi.

Ministan Shari'a, Abubakar Malami

Shi ma ya yi rawar gani a wannan gwamnatin, sai dai kuma shugaban kasar zai iya canja shi a kowanne lokaci.

Ministan Man Fetur, Dr. Ibe Kachikwu

Ibe Kachikwu, dan asalin jihar Delta ne, shi ma ya yi rawar gani a na shi bangaren, sai dai kuma ana ganin matsalar da ke tsakanin sa da manajan kamfanin man fetur na kasa Maikanti Baru, zai iya shafar kujerarsa.

Ministan Tattalin Arziki, Sanata Udoma Udo Udoma

Ya yi wa gwamnati kokari a na shi bangaren, sai dai kuma shi ma akwai rade-radin Sanata Godswill Akpabio zai iya karbar kujerar shi.

Ministan cikin gida, Janar Abdulrahman Dambazau

Da akwai yiwuwar ministan da shi da ministan Abuja, za su iya yin nasarar bin shugaban kasar a karo na biyu.

Sannan akwai wasu ministocin da ba a san halin da suke ciki ba, saboda haka zai yi wuya a bayyana idan zasu iya bin shugaban kasar ko baza su iya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel