2019: Jiga-jigan PDP da yawa sun ci amanan jam'iyyar a Gombe - Dankwambo

2019: Jiga-jigan PDP da yawa sun ci amanan jam'iyyar a Gombe - Dankwambo

Gwamna Ibrahim Dankwambo na jihar Gombe ya koka kan yadda mafi yawancin jiga-jigan jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP a jihar Gombe suka rika cin amanar jam'iyyar yayin babban zaben 2019 da aka kammala.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ta shafinsa na kafar sada zumunta na Facebook a ranar Asabar 6 ga watan Afrilu.

Sai dai ya dau alwashin zai cigaba da kasance a cikin jam'iyyar inda ya kira kansa 'mai kishin jam'iyya'.

Kalamansa: "Mutane da yawa a jihar Gombe sun ci amanar jam'iyyar mu mai martaba amma komi yana da lokacinsa. Duk da cewa cin amanar da su kayi ya min zafi, hakan ya sa na kara kaunar jam'iyyar PDP.

"A matsayina na mai kishin jam'iyya, ban taba fice wa daga jam'iyyar PDP ba ko da lokacin da ake yayin ficewa daga jam'iyyar a Arewa a 2015. Za mu ga sakayya a gaba."

DUBA WANNAN: Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Kazalika, Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abiodun Olujimi ta ce kayen da PDP da sha a jihar Ekiti a zaben da ta gabata wani koma baya na wucin gadi ne ga jam'iyyar.

A cewar ta, rashin jituwa tsakanin mambobin PDP na jihar da magudi da jam'iyyar APC tayi ne ya janyo wa PDP shan kaye a jihar.

Ta kuma ce tayi imanin cewa jam'iyyar za ta dawo da martabar ta a jihar cikin kan-kanin lokaci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel