Yanzu-yanzu: Daliban Kano 3 sun rasa rayukansu

Yanzu-yanzu: Daliban Kano 3 sun rasa rayukansu

Daliban jami'ar Kimiya da fasaha dake Wudil KUST, jihar Kano uku sun rasa rayukansu sakamakon wani mumunan hadarin mota da ya auku da su yayinda wasu biyu suka jikkata.

Tabbatar da faruwan, mataimakin jami'in hulda da jama'a na jami'ar, Mallam Abdullahi D. Abdulahi, ya bayyana cewa hadarin ya faru ne a kauyen Tudun Gusau dake karamar hukumar Takai da jihar Kano ranar Juma'a.

Abdullahi ya ce daliban su biyar suna tafiya cikin wata mota kirar Peugeot 206, inda sukayi kokarin gujewa rami sai motar ta kwacewa direban ya ci karo da wata mota mai zuwa a gabansa.

KU KARANTA: Yan Kannywood sun shirya liyafa ta musamman domin murnar nasarar Buhari

Yace: "Dalibai biyu sun mutu take a wajen yayind a na ukun ya rasu a asibiti. An kai saur biyu asibitin Aminu Kano da ke birnin jihar."

"Daya daga cikinsu wanda raunukan da ya samu basu da yawa tuni an sallameshi amma daya na asibiti har yanzu."

Ya kare da cewa an mika gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu ga iyalansu domin jana'iza.

Masu ruwa da tsaki a masana'antar fina-finan Kannywood sun shirya liyafa ta musamman domin murnar nasarar shugaban Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, da duk zababbun mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, yau.

A jawabin da daya daga cikin diraktocin masana'antar, Aminu Saira, yayi, ya ce mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ne zai zama babban bako a taron.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel