Takarar shugabancin majalisa: Sanatocin Kano sun goyi bayan Lawan

Takarar shugabancin majalisa: Sanatocin Kano sun goyi bayan Lawan

- Sanatoci uku daga jihar Kano sun goyi bayan takarar Sanata Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa

- Sanatocin uku sune Barau Jibrin, Kabiru Ibrahim Gaya da zababen Sanata Mallam Ibrahim Shekarau

- Sanatocin sun ce sun goyi bayan Lawan ne saboda dadewarsa a majalisa da kwarewarsa wurin aiki

Sanatoci uku daga jihar Kano sun sanar da goyon bayan su ga jagorar majalisar, Sanata Ahmad Lawan domin zama shugaban majalisar dattawa karo na tara.

Sanatocin uku Barau Jibrin, Kabiru Ibrahim Gaya da zababen Sanata Mallam Ibrahim Shekarau sun sanar da hakan ne lokacin wata ziyara da suka kai gidan Shekarau.

Takarar shugabancin majalisa: Sanatocin Kano sun goyi bayan Lawan

Takarar shugabancin majalisa: Sanatocin Kano sun goyi bayan Lawan
Source: UGC

DUBA WANNAN: Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Sunyi ikirarin cewa Lawan shine dan majalisa da yafi dadewa a majalisar kuma yana da kwarewa a kan yadda harkokin majalisar ke gudana saboda haka idan za a bi yadda ake tafiyar da harkokin majalisa a kasashen duniya shine ya dace ya zama shugaba.

The Nation ta ruwaito cewa sanatocin sun sanar da goyon bayansu ga Lawan ne lokacin da Barau Jibrin wadda shine sakataren kamfen din Lawan ya jagorancin wasu mambobin kamfen din zuwa gidan zababen sanata Shekarau.

Sanata Jibrin ya ce: "Ana zaben shugabanin majalisa ne bisa tsarin da kasashen duniya keyi wurin zaben shugabani. Abinda mu kayi amfani da shi kenan.

"A kowanne majalisa, ana la'akari da mukami, da dadewa da majalisa saboda haka da an zo zabe, jam'iyyar da ke da rinjaye tana zaben dan majalisa mafi dadewa da kwarewa ne domin ya yi jagoranci.

"Yanzu, Ahmed Lawan shine dan majalisar da ya fi kowa dadewa a majalisa karo na tara. Ya yi majalisar wakilai sau biyu, sannan ya yi sanata sau hudu. Hakan na nuna cewa shine mafi kwarewa da dacewa ya jagoranci majalisar idan za a bi yadda ake zabe a kasashen duniya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel