Wata sabuwa: Kotu ta samu sabbin hujoji a kan tuhumar almundahar N1.35bn da ake yiwa Sule Lamido

Wata sabuwa: Kotu ta samu sabbin hujoji a kan tuhumar almundahar N1.35bn da ake yiwa Sule Lamido

- Kotun Tarayya da ke Abuja ta samu karin hujoji daga Hukumar EFCC a kan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido

- Sauran wadanda ake tuhuma tare da shi sun hada da yayansa biyu, Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido, kamfanoni biyu da wani Aminu Wada Abubakar

- An tuhumar tsohon gwamnan da taimakon sauran mutanen da damfarar jihar zunzurutun kudi Naira Bilyan 1.35

Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja, a ranar Juma'a 5 ga watan Afrilu ta samu karin takardu daga Hukumar Yaki da Masu Yiwa Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC a matsayin hujoji a kan tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da wasu da ake tuhuma.

Ana dai tuhumar Lamido ne tare da yaransu biyu Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sauran da ake tuhumar tare da shi sun hada da wani Aminu Wada Abubakar da wasu kamfanoni biyu; Bamaina Holdings Limited da Speeds International Limited.

DUBA WANNAN: Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Wata sabuwa: Kotu ta samu sabbin hujoji a kan tuhumar almundahar N1.35bn da ake yiwa Sule Lamido

Wata sabuwa: Kotu ta samu sabbin hujoji a kan tuhumar almundahar N1.35bn da ake yiwa Sule Lamido
Source: Twitter

Idan ba a manta ba dai Hukumar EFCC tana tuhumar su ne da laifin damfarar jihar Jigawa zunzurutun kudi Naira Bilyan 1.35.

Takardun da aka gabatarwa kotu sun hada da umurnin kotu na tilasta wakilin Bankin UBA, Longi Tupkop ya gabatar da shaidan bude asusun ajiya na kamfanin gine-gine na Dantata and Sowoe, sunayen wadanda ke da hannun jari a kamfanin da wasu bayanai na kamfanin.

Shaidan da Tupkop ya bayar da kotu ya nuna hada-hadar kudin da akayi daga ranar 23 zuwa 26 na watan Afrilun 2013 ciki har da kudi N35,627,061.85.

Mai bayar da shaidan ya ce: "A ranar 3 ga watan Afrilun 2013 an gabatar da cheque kuma an fitar da kudi amma an dawo da cheque din kuma an mayar da kudadin cikin asusun ajiyar saboda ba a tabbatar da izinin fitar da kudaden ba. Sai dai a ranar 26 ga watan Afrilun 2013 an sake dawowa da cheque din kuma an fitar da kudaden."

Kotun ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranakun 20, 21 da 22 na watan Mayun 2019 karkashin jagorancin alkaliyar kotun, Ijeoma Ojukwu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel