Yan Kannywood sun shirya liyafa ta musamman domin murnar nasarar Buhari

Yan Kannywood sun shirya liyafa ta musamman domin murnar nasarar Buhari

Masu ruwa da tsaki a masana'antar fina-finan Kannywood sun shirya liyafa ta musamman domin murnar nasarar shugaban Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, da duk zababbun mambobin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, yau.

A jawabin da daya daga cikin diraktocin masana'antar, Aminu Saira, yayi, ya ce mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ne zai zama babban bako a taron.

Sauran bakin da aka gayyata sune uwargidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, abokiyarta uwaridar mataimakin shugaban kasa, Dolapo Yemi Osinbajo, shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, da ministan sufuri, Rotimi Amaechi da sauran jigogin jam'iyyar.

Yan Kannywood sun shirya liyafa ta musamman domin murnar nasarar Buhari
Yan Kannywood sun shirya liyafa ta musamman domin murnar nasarar Buhari
Source: Facebook

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi na musamman a kasar Urdu (Hotuna)

Game da cewar Saira, za'a gudanar da liyafar ne a Transcorp Hilton dake Abuja kuma dukkan masu fada a ji na masana'antar za su halarta.

Saira yace: "Taron zai karbi bakuncin dukkan manyan Kannywood da ya kunshi Ali Nuhu, Sadiq Mafia, Abdul Amart, Halima Atete, Rukayya Dawayya da dukkan jaruman masana'antar da suka goyi bayan APC yayin yakin neman zabe."

Babban mai jagoran shirin, Ibrahim Maishinku, ya bayyana cewa taron zai bayyana yan masana'antar da ke karkashin tutar masu son cigaban kasa.

Ya ce Kannywood ta taka rawar gani wajen goyon bayan Buhari da Osinbajo kuma suna kyautata zaton za'a mayar musu da alkhairi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel