Kuma dai! Dan sanda ya bindige mijin mai cikin wata takwas

Kuma dai! Dan sanda ya bindige mijin mai cikin wata takwas

Wani dan sanda ya bindige dan Achaba mai suna Odeh Stephen, ranar Alhamis, 5 ga watan Afrilu a unguwar Ahoad, jihar Rivers.

Marigayin Stephen dan asalin karamar hukumar Sagbama da ke jihar Bayelsa ya gamu da ajalinsa yayinda yan sanda suka tsayar da su domin duba su.

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa: "Ya tsaya a wajen yan sanda. Yayinda yake tafiya domin yi musu magana, sai daya daga cikin yan sandan ya harbesa. Abin dadin shine abokan aikin dan sandan sun tsareshi nan take."

KU KARANTA: Yadda iyaye suke sayar da 'ya'yansu mata ta shafin Facebook a Najeriya

Wata majiya ta kara da cewa marigayin mijin wata mata mai cikin watanni takwas ne.

"Abin ya faru tsakanin garin Ahoad da Mbiama a jihar Rivers. Labarin da muka samu ya nuna cewa dan sandan da wanda ya kashe duka yan karamar hukumar Sagbama dake jihar Bayelsa ne."

"Yanzu matsalan shine yadda za'a fadawa uwargidarsa mai juna biyun wata takwas wannan labari."

An tuntubi kakakin hukumar yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni, amma bai amsa kiransa ba.

A bangare guda, Wani mai tabin hankali ya hallaka jami'in dan sanda mai suna, Sajen Abu, da ke aiki a ofishin hukumar dake Omu-Aran, jihar Kwara.

Majiyar Legit.ng ta samu labarin cewa dan sandan na cikin ofishinsa ne yayinda mahaukacin mai suna, femi Adefila, wanda ke rike da adda da wasu makamai ya afka masa a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel