Assha: Malamin Jami'a ya cinna wa kansa wuta

Assha: Malamin Jami'a ya cinna wa kansa wuta

Wani malamin makaranta a tsangayar nazarin lissafi na Jami'ar Ibadan ya cinna wa kansa wuta kuma hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Malamin mai suna Mr A.O Subair ya cinnawa kansa wutan ne a jiya Juma'a 5 ga watan Afrilu a gidansa da ke Phillipson Road a cikin jami'ar.

Tuni dai an birne shi a makabartar Akinyele bisa koyarwan addinin musulunci.

DUBA WANNAN: Wata mata ta fadi matacciya yayin fada da kishiya a Kano

Assha: Malamin Jami'a ya cinna wa kansa wuta

Assha: Malamin Jami'a ya cinna wa kansa wuta
Source: Twitter

Silverbird TV ta ruwaito cewa malamin ya yi murabus daga aikinsa a jami'an ba tare da wata kwakwaran dalili ba amma bai riga ya kwashe kayansa daga gidansa na jami'an ba kwatsam sai ya kashe kansa.

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya rabu da iyalansa kuma yana fuskantar kallubale a wurin aikinsa.

A yayin da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin a hirar wayar tarho, Shugaban kungiyar malamai, ASUU na jami'ar, Farfesa Deji Omole ya ce rasuwar malamin abin bakin ciki ne kuma babban rashi ga kungiyar.

Omole ya ce, "An sanar da mu cewa gidansa na konewa ne kuma munyi kokarin ceto rayuwansa amma hakan bai yiwu ba."

Omole ya shawarci mambobin kungiyar su rika sanar da juna halin da suke ciki inda ya ce, "kadaici na tsananta damuwa wanda hakan na iya saka mutum ya kashe kansa."

Malamin ya rasu ya bar yara uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel