Sau 5 ana min tayin kujerar Minista a lokacin Obasanjo da 'Yar'adua - Buba Galadima

Sau 5 ana min tayin kujerar Minista a lokacin Obasanjo da 'Yar'adua - Buba Galadima

- Sau uku Obasanjo ya na bani kujerar Minista ina ce wa ba na so

- 'Yar'adua har kujerar Ministan Abuja ya bani na ce bana so

- 'Ya ta kuma kamar diya ce a gurin shugaba Buhari

Daya daga cikin manyan masu kalubalantar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma jigo a jam'iyyar PDP, Buba Galadima, ya bayyana dalilin shi na kalubalantar gwamnatin shugaban kasar, inda ya ce shi ba ya bukatar gwamnatin Buhari ta bashi wani matsayi a majalisa, Bayan haka kuma Galadima ya bayyana dagantakar shugaban kasa Muhammadu Buhari da diyarshi, sannan ya bayyana kudurin shi na fatan jam'iyyar PDP ta kada Buhari a zaben da za ayi nan gaba.

Da aka tambayeshi akan cewar mutane suna ganin kamar yana zagin gwamnatin shugaba Buhari saboda ba a bashi mukami ba, sai ya ce:

"Ban so na amsa wannan tambayar ba, amma ina daya daga cikin mutane tara da suka samar da jam'iyyar APC, wasu tambayoyin da mutane su ke yi suna bani dariya, bama kuma wannan ne matsalar ba, matsalar ita ce yadda mutane suke saurin mance abubuwan.

Sau 5 ana bani kujerar Minista a lokacin Obasanjo da 'Yar'adua - Buba Galadima

Sau 5 ana bani kujerar Minista a lokacin Obasanjo da 'Yar'adua - Buba Galadima
Source: Depositphotos

"Mutane sun manta da cewar nine mutum daya dana addabi gwamnatin tsohon shugaban kasa Obasanjo da marigayi 'Yar'adua sannan ta dalili na ne ya sa suka gabatar da wasu manyan aiyuka a kasar nan. Saboda haka abinda nake yi wa gwamnatin shugaba Buhari bai ko kama kafar abinda na yi wa Obasanjo da Yar'adua ba. Mutane duk sun mance da wannan abubuwan da su ka faru a baya, ko wa yana yi mini kallon mutumin banza. Obasanjo, 'Yar'adua, da Jonathan sun kama ni har sau biyar, sun daure ni. Abin ya na bani dariya a duk lokacin da na ji mutane sunce ina zagin Buhari saboda bai bani mukami ba. Ya na nan a rubuce gwamnatin Obasanjo ta ba ni kujerar minista har sau uku, Yar'adua ya nemi da na karbi kujerar Ministan Abuja, amma du ka na ce bana so.

"Sannan kuma Wadanda su ke cewa diyata ta na aiki da shugaba Buhari, su na yi mini ba'a ne. 'Diyata kamar diya ce a wurin shugaba Buhari, saboda a al'ada duk wanda ya yi wa mace walittaka kamar uba ne ga wannan yarinyar. 'Ya ta tana da tarihi da shugaba Buhari. Ko lokacin da ta gama karatun ta a birnin Landan, ni da Buhari muka je mata bikin yaye dalibai; lokacin da za ayi aurenta, Buhari ne ya yi mata walicci. Lokacin da ta haihu dan ta na farko sunan Buhari ta saka mishi.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

"Sannan kuma diyata cikakkiyar 'yar Najeriya ce, ta yi aiki da mataimakin shugaban kasa tukuru domin ganin shugaba Buhari ya hau mulki, a takaice ma ita ce wacce ta jagoranci kamfen din shi a birnin tarayya. A ga ni na idan za a biya ta da irin wahalar da ta yi, kamata ya yi a bata matsayin minista. Diyata ta na da kwalin digiri guda biyu, da kuma ta na da kwaalin digirin-digirgir guda uku.

"Babu wani mutum a cikin 'yan majalisar Buhari da ya ke da irin takardun ta, hatta shi shugaban kasar. Amma kuma duk da haka an hana ta wani babban mukami," in ji Buba Galadima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel