Yadda iyaye suke sayar da 'ya'yansu mata ta shafin Facebook a Najeriya

Yadda iyaye suke sayar da 'ya'yansu mata ta shafin Facebook a Najeriya

- Ana amfani da shafin yanar gizo na Facebook wurin tallata bayi a Najeriya

- Iyaye na sayar da 'ya'yansu mata domin biyan bashin kudin

- Ana amfani da matan ta kowacce hanya domin biyan bukata

Al'adar sayar da mata tun suna kanana, wata al'adace da ta samo asali a wurin al'ummar Becheve, da ke kauyen Obanliku cikin jihar Cross River. Iyaye suna amfani da yara mata wurin musayar abinci, dabobbi, ko kudi. Irin wadannan matan su suke kira da matan kudi.

Sai dai yanzu wani cigaba da al'ummar yankin suka samu shine, suna amfani da shafin yanar gizo na facebook, wurin tallata 'ya'yan na su. Lokuta da dama akan sayar da su ga tsofaffin mutane, kuma da an sayar da ke, shikenan kin zama tamkar baiwa ga wannan mutumin har bayan rayuwarki.

Yadda 'yan Najeriya ke sayar da mata ta shafin Facebook
Yadda 'yan Najeriya ke sayar da mata ta shafin Facebook
Source: Twitter

Mutanen su suke zabar abinda matan zasu yi musu. Wasu suna amfani da su wurin kwanciya, wasu kuma suna mayar da su 'yan aikin gida da zuwa aikin gona, wasu ko zaben suzasu fada miki wanda zaki zaba.

Wata yarinya mai suna Monica ta bayyanawa 'yan jarida yadda mahaifinsu ya sayar da su ba tare da son ransu ba, domin ya biya wani bashi da ake binshi. Monica ta ce ita da kanwarta anyi musu auren dole da mutanen da ba su san su ba, kuma tsofaffi.

Ta ce: "Mahaifinmu bai san da wani abu Facebook ba har sai lokacin da yayanmu ya siyo mishi wayar salula ta zamani, sannan ya roke shi akan ya fara amfani da Facebook, ya na saka hotunan mu a duk lokacin da ya ke so.

"Ya na siyo mana sabbin kaya ya ba mu saka kafin ya dauke mu hoto ni da kanwata."

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

Monica ta ce ta gudu daga gidan mijin da aka yi mata auren dole ta koma gidan wata kawarta, shekara daya bayan aurenta da mutumin.

A al'adar mutanen Becheve, iyaye yaarinya su ne suke kai yarinyar gurin wanda zai saye ta. Amma a 'yan watannin na iyayen da su ke son kudi ido rufe, su kan yi amfani da shafin Facebook wurin sanya hotunan 'ya'yan na su domin masu kudin yankin su duba irin wacce su ke so su saya.

Wani mai fada aji a garin Ogbakoko, Magnus Ejikang, ya bayyanawa manema labarai cewa: "Sunayin wannan al'ada ce saboda karawa maza kwarin guiwa a yankin na Becheve. Iya yawan matan da kake da su iya girman da mutane za su dinga baka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel