Za a samar da karin yankuna a jihar Bauchi

Za a samar da karin yankuna a jihar Bauchi

- Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana shirin da ake yi na aiwatar da wani doka don samar da sabbin yankuna da kauyuka

- Jawabin Gwamna Mohammed Abubakar ya nuna cewa dokar wanda za a gabatar ga majalisar dokoki na daga cikin kokarin da ake na kara sanya hukumomin gargajiya a harkar gwamnati, musamman ta fannin tsaro

- Shugaban kwamitin da aka kafa kan haka, Justis Dahiru Saleh, yace sun bayar da shawarar samar da sabbin yankuna 50 da sabbin kauyuka 225

Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar ya bayyana shirin da ake yi na aiwatar da wani doka don samar da sabbin yankuna da kauyuka.

A wani jawabi daga sakataren labaransa, Abubakar Al-Sadique, ya ayyano gwamnan na bayyana hakan a lokacin da ya karbi rahoton kwamitin da ke sake duba batun samar da yankuna da kauyuka daga gwamnatin Isah Yuguda.

A cewar jawabin, dokar wanda za a gabatar ga majalisar dokoki na daga cikin kokarin da ake na kara sanya hukumomin gargajiya a harkar gwamnati, musamman ta fannin tsaro.

Za a samar da karin yankuna a jihar Bauchi

Za a samar da karin yankuna a jihar Bauchi
Source: Depositphotos

Gwamna Abubakar yace an ba kwamitin damar aiwatar da aikin kai tsaye.

A tuna cewa Abubakar ya kafa kwamitin domin sake duba shirin ne biyo bayan lamarin da ya yi sanadiyar da majalisar dokokin ta rushe sabbin yankuna a farkon shekarar 2015.

KU KARANTA KUMA: Onnoghen ya mika takardar murabus ga fadar shugaban kasa

Shugaban kwamitin, Justis Dahiru Saleh (mai ritaya), yace sun bayar da shawarar samar da sabbin yankuna 50 da sabbin kauyuka 225.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel