Onnoghen ya mika takardar murabus ga fadar shugaban kasa

Onnoghen ya mika takardar murabus ga fadar shugaban kasa

Rahotanni sun kawo cewa, Alkalin Alkalan Najeriya Walter Onneghen, wanda aka dakatar, ya mika takardar murabus zuwa ga fadar Shugaban kasar Najeriya.

Fadar Shugaban kasa bata tabbatar da karban wasikar murabus din ba daga hannun Onnoghen, sa’o’i 24 bayan rade-radin yayi fice.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Alkalan kotun koli sun gabatar da wasika Onnoghen ga Shugaban ma’aikatan Shugaban kasar, Malam Abba Kyari.

NAN, ta tattaro cewa Alkalan sun iso fadar Shugaban kasa yan mintuna kadan bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Abua zuwa kasar Jordan don halartan taron kungiyar tattalin arziki na duniya a ranar Alhamis.

Onnoghen ya mika takardar murabus ga fadar shugaban kasa

Onnoghen ya mika takardar murabus ga fadar shugaban kasa
Source: Twitter

Wata majiya daga fadar Shugaban kasa ta tabbatar wa NAN cewa shugaba Buhari, kafin tafiyarsa ya samu shawarwari daga maalisar Alkalai na kasa kan korafi game da Onnoghen da kuma mukaddashin Shugaban Alkalai, Justis Tanko Muhammed.

KU KARANTA KUMA: Maganar boye ta fito fili: An gano dalilin da yasa Ganduje ya kada Abba a Kano

Shugaban ma’aikatarsa, Mallam Abba Kyari ne ya gabatar da rahoton ga Shugaban kasa, wanda ya samu rakiyan Atoni-anar kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami, da misalin karfe 2:20 na wannan ranar.

Duk kokari na ji daga bakin kakakin Shugaban kasa, Mista Femi Adesina da Mallam Garba Shehu kan lamarin yaci tura yayinda su dukka biyun ke wajen kasar bisa aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel