An tsare Almajirai biyu kan zargin kisan dan maigida

An tsare Almajirai biyu kan zargin kisan dan maigida

Hukumar yan sandan jihar Kano ta kaddamar da bincike kan al'amarun zargin kisan wani dan shekara 9 mai suna, Najib Kamal, da wasu Almajirai biyu sukayi a garin Kuntau, karamar hukumar Gwale dake jihar.

An tsinci gawar Najib ne rataye kan kofa a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, kuma an damke mutane biyu da ake zargi da kisan.

Almajiran masu suna Sani Musa da Maharazu Yusuf sun kasance yan aike a gidansu Najib ne gabanin faruwan wannan abu.

Jaridar Daily Trust ta samu labarin cewa Almajirin ya samu sabani da matar maigidan kan rashin ji da tace yakeyi kuma sakamakon haka ta hanashi abinci. Sai Sani ya bace daga gidan na tsawon kwanaki uku ba'a gansa ba, amma ya dawo a ranar da abin ya faru.

Mahaifyar, Malama Na’ima Rabi’u, ta bayyana cewa tana cikin gida bata san abinda ya faru ba sai da yamma da ta fara neman yaronta, sai aka fada mata ya mutu.

Tace: "Ina barci a dakin sama kuma suna wasa, da yamma sai na bukaci a kira min shi da sauran yan'uwansa tunanin cewa suna wasa, sai dai aka kawo min gawar dana Najib.

Da na tambayi kaninsa Nabil shin me ya samu dan'uwansa, ya fada min cewa sun tsinceshi rataye a kan kofa kuma ya kira daya daga cikin almajiran da ke masu wanki sunansa Maharazu domin ya saukeshi."

"Maharazu ya sauko kuma ya saukar da shi, sannan ya shiga da shi daya daga cikin dakunan. Sannan ya hau gidan sama ya karbi abinci kuma ya tafi ba tare fada min komai ba"

Ta ce sabanin Ita, Sani (Almajirin) mairgayin da dan'uwansa, babu kowa a gidan. Yayinda mahaifin, Malan Kamal Aminu Bala, ya kai gawar asibiti, an tabbatar da cewa ratayeshi akayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel