Da duminsa: Onnoghen ya bayyana dalilinsa na yin murabus

Da duminsa: Onnoghen ya bayyana dalilinsa na yin murabus

Adegboyega Awomolo, lauyan Alkalin alkalan Najeriya da aka dakatar, Justice Walter Onnoghen ya yi bayanin cewa Onnoghen ya yi murabus ne saboda kare martabar bangaren shari'a na Najeriya.

The Nation ta ruwaito cewa lauyan ta tabbatar da cewa Onnoghen ya yi murabus a ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu.

Awomolo ya ce ya yi magana da Alkalin alkalan na Najeriya da aka dakatar kuma ya fada masa cewa ya yi murabus din ne saboda kare martabar bangaren shari'a.

Da duminsa: Onnoghen ya bayyana dalilin da yasa ya yi murabus

Da duminsa: Onnoghen ya bayyana dalilin da yasa ya yi murabus
Source: UGC

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Ya ce: "Yanzu na yi magana da shi. Ya tabbatar min da cewa ya yi murabus a jiya.

"Ya ce ya yi murabus ne saboda kare martabar bangaren shari'a."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel