An tsare wan mai gadi kan laifin lalata yar shekara 12

An tsare wan mai gadi kan laifin lalata yar shekara 12

Wata kotun Majistare da ke Ikeja a ranar Juma’a, 5 ga watan Afrilu ta yi umurnin rufe wani mai gadi dan shekara 32 mai suna Dennis Nba, bisa zargi yi wa wata yar shekara 12 fyade a kurkuku, har sai an saurari shawara daga daraktan hukunta jama’a na jihar Legas.

Majistare Olufunke Sule-Amzat, wacca ta ki bayyana ra’ayinst akan roko da mai laifin yayi, ta bada umurni cewa a rufe mai laifin a gidan kurkukun kirikiri.

Garafini ya umurci hukumar yan sanda da ta gabatar dakwafin takardunsu akan lamarin zuwa ga hukumar DPP.

Mai shari’an ta daga sauraran karan har zuwa ranar 24 ga watan Yuli.

An tsare wan mai gadi kan laifin lalata yar shekara 12

An tsare wan mai gadi kan laifin lalata yar shekara 12
Source: Twitter

An kama Nba, wanda ke da zama a hanyar Ikoba a Monkey-Village, Maza-Maza, Legas, da laifin fyade.

A baya, mai gabatar da kara, ASP Benson Emurhi, ya fada ma kotun cewa mai laifin ya aikata laifin ne a ranar 17 ga watan Maris a gidansa.

Emuerhi yayi zargin cewa mai laifin, wanda ke aikin gadi a gidan yarinyar, yayi mata fyade.

KU KARANTA KUMA: Muhawarar kasafin kudi: Majalisar wakilai tayi fatali da bukatar kashe N29m wajen gyaran bandakuna

Ya bayyana cewa mahaifin yarinyar ne ya kai karan lamarin ofishin yan sanda sannan daga baya aka tura karan zuwa ga sashin kare yancin jinsi na rundunar yan sandan jihar Legas, reshen Ikeja, don cigaba da bincike.

Ya bayyana cewa laifin ya saba ma sashin 137 na dokar aikata miyagun ayyuka na jihar Legas, 2015.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel