Hukumar NIMC ta fara yiwa Almajirai rajista a Kano

Hukumar NIMC ta fara yiwa Almajirai rajista a Kano

Hukumar da ke kula da kuma samar da lambar shaidan zaman dan kasa (NIMC) reshen jihar Kano ta fara yi wa almajirai da ke jihar Kano rajista.

Shugaban sashin hulda da jama'a na hukumar, Mr Loveday Ogbonna ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a a babban birnin tarayya, Abuja.

Ogbonna ya ce an fara hakan ne kamar yadda ya ke cikin tsarin hukumar na samar da katin dan kasa ga dukkan 'yan Najeriya tare da sanya bayanansu a cikin rajistan hukumar.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Hukumar NIMC ta fara yiwa Almajirai rajista a Kano
Hukumar NIMC ta fara yiwa Almajirai rajista a Kano
Source: Instagram

Ya ce shugaban hukumar na jihar Kano, Mr Sanusi Muhammad ya sanar da cewa an fara samun nasara a cikin kwanaki shida da aka fara gudanar da aikin rajistan a Kano.

Ya ce an samu nasarar aikin ne saboda irin gudunmawa da hadin kai da gwamnatin jihar Kano ke bawa hukumar hakan ya sanya mazauna jihar su ke maraba da aikin.

Ya ce yiwa Almajirai rajistan zai taimaka wurin gane mazauna jihar kuma hakan zai taimaka wurin rage ayyukan barna da kare safarar mutane a jihar.

"Za a cigaba da fadada aikin yiwa Almajirai rajistan NIN zuwa sauran sassan jihar tare da yiwa kananan yara rajista kamar yadda ake yi a jihohin Najeeiya 36 da Abuja a halin yanzu," inji shi.

Muhammad ya mika godiyarsa bisa irin gudunmawar da gwamnatin jihar Kano da kananan hukumomi ke basu kuma ya yi kira ga 'yan Najeriya da sauran masu zama a kasar su yiwa yaransu rajista.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel