Ban yi danasanin faduwa zaben sanata ba - Ajimobi

Ban yi danasanin faduwa zaben sanata ba - Ajimobi

Gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, a ranar Juma’a, 5 ga watan Afrilu, yace babu wani dalili da zai sa shi danasani ko damuwa akan faduwar da yayi a kudirinsa na neman kujerar sanata da kuma rashin mika mulki ga dan jam’iyyarsa na All Progressives Congress (APC).

Yace Allah mai iko ne ya bashi dammar mulki sau biyu tare da samun nasarori fiye da tsammani, yace bai ga dalilin da zai sa yayi nadama ba akan rashin samun nasara a zaben sanata.

Gwamnan ya fadi hakan ne a bikin zagayowar ranar haihuwar matarsa Misis Florence Ajimobi, karo na 60, wanda aka gudanar a gidan Gwamnati a Ibadan.

Ban yi danasanin faduwa zaben sanata ba - Ajimobi
Ban yi danasanin faduwa zaben sanata ba - Ajimobi
Source: Depositphotos

Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai matar mataimakin shugaban kasa, Misis Dolapo Osinbajo; matar gwamnan jihar Ekiti, Erelu Bisi Fayemi; Takwararta na jihar Imo, Misis Nkechi Okorocha; Matar zababben gwamnan jihar Ogun, Misis Bamidele Abiodun; da matar tsohon gwmnan jihar Osun, Misis Sherifat Aregbesola, da sauran manyan baki.

KU KARANTA KUMA: Kotun kolin Najeriya ta shiga halin rudani bisa rahoton ajiye aiki na Alkalin Alkalai

Bayan kasancewa a mulki har na tsawon shekaru takwas, wanda ya kafa tarihin jihar, gwamnan ya bayyana cewa Allah ya dube shi da idon rahama don sake kafa tarihin jihar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel