Muhawarar kasafin kudi: Majalisar wakilai tayi fatali da bukatar kashe N29m wajen gyaran bandakuna

Muhawarar kasafin kudi: Majalisar wakilai tayi fatali da bukatar kashe N29m wajen gyaran bandakuna

Kwamitin majalisan wakilai kan harkokin yawon bude ido da al’adu, a ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu ta nemi bayani daga babbar manaja gidan wasar kwaikwayo na kasa wato 'National Theatre', Dr. Stella Oyedepo, akan kashe kudi naira miliyan 29 wajen gyaran bandakuna.

Oyedepo yayin da take sake duba ga kasafin kudi na 2018, ta fada ma yan majalisar cewa ta kashe naira miliyan 29 wajen gyaran bandakunan cibiyar.

Yan majalisan basu ji dadin hakan ba ganin kashe makudan kudade da tayi wajen gyaran bandakuna.

Shugaban kwamitin, Omoregie Ogbeide-Ihama yace: “akwai bukatar a gabatar da binciki matuka akan yanda kika kashe har naira milyan 29 wajen gyaran bandakuna.”

Muhawarar kasafin kudi: Majalisar wakilai tayi fatali da bukatar kashe N29m wajen gyaran bandakuna

Muhawarar kasafin kudi: Majalisar wakilai tayi fatali da bukatar kashe N29m wajen gyaran bandakuna
Source: Depositphotos

A martanin da ta bayar, Oyedepo tace: “Bandakuna sun kai 500 a harabar kuma hakan yasa wajen ya kasance da rashin kyan gani saboda mumunan yanayi da suka kasance a ciki. Abunda muka yi shine mun sake canja kayayyakin bandakin ne gaba daya saboda harabar yayi kyau.”

KU KARANTA KUMA: Kotun kolin Najeriya ta shiga halin rudani bisa rahoton ajiye aiki na Alkalin Alkalai

A hukuncinshi, shugaban kwamitin, yace: “Kwanan nan manajan ta koma bakin aiki, ana iya yi mata rangwame amman dole ta hada takardun ta don bai wa kwamitin damar gudanar da aikinta a tsanaki.”

A halin da ake ciki dai, kwamitin ta fidda mai wakilin babban manajan hukumar kula da fannin zane-zane na kasa, Mista Richard Ovie daga dakin ganawar bisa rashin iya wakilci.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel