Murabus din Onnoghen: Ko uffin fadar shugaban kasa ba tayi ba har yanzu

Murabus din Onnoghen: Ko uffin fadar shugaban kasa ba tayi ba har yanzu

Har yanzu, fadar shugaban kasa ba tace uffin kan wasikar murabus da tsohon alkalin alkalai, Walter Onnoghen, ya aika mata ba, kimanin sa'o'i 24 bayan rahotanni sun yadu kan haka.

Ma'aikatar dillancin labaran Najeriya NAN ta samu labarin cewa wasikar murabus din Onnoghen ta shiga hannun shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Abba Kyari, daga hannun wasu alkalan kotun koli.

Amma an samu labarin cewa alkalai sun dira fadar shugaban kasa mintuna kalilan bayan tafiyar shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar Urdu domin halartan taron kungiyar tattalin arzikin duniya.

Wata majiya da fadar shugaban kasa ta tabbata da cewa kafin tafiyarsa Urdu, shugaba Buhari ya samu wasikar majalisar kolin shari'a kan Onnoghen da Tanko Muhammad.

Abba Kyari da ministan shari'a, Abubakar Malami sun mikawa shugaban kasa wasikar misalin karfe 2:20 na rana.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

Mun kawo muku cewa Bisa ga shawarar majalisar koli ta shari'a NJC, komai ya kankama domin tabbatar da mukaddashin shugaban Alkalai, Ibrahim Tanko Muhammad, a matsayin Alkali alkalai na din-din-din.

Ana kyautata zaton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai karbi shawarar majalisar Shari'a ta kasa.

Amma rahoto ya nuna cewa Buhari na tantaman karbar shawarar matsaliyar kolin kan cewa a yiwa tsohon alkalin alkalai, Walter Onnoghen, ritayar dole maimakon hukunta shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel