Kotun kolin Najeriya ta shiga halin rudani bisa rahoton ajiye aiki na Alkalin Alkalai

Kotun kolin Najeriya ta shiga halin rudani bisa rahoton ajiye aiki na Alkalin Alkalai

Kotun koli ta Najeriya ta shiga cikin halin rudani biyo bayan rahoton dake yawo a kafafen sadarwa na cewa wai Alkalin Alkalai da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar, mai sharia Walter Onnoghen ya yi murabus daga aiki.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a dalilin wannan rudani yasa kotun kolin ta gagara tabbatar da gaskiya ko akasin wannan rahoto, wanda a yanzu haka yana shan muhawar a tsakanin yan Najeriya tare da tofa albarkacin bakinsu.

KU KARANTA: Kalli yadda Buhari ya shiga kasar Jordan

Kotun kolin Najeriya ta shiga halin rudani bisa rahoton ajiye aiki na Alkalin Alkalai
Onnoghen
Source: UGC

Ofishin babbar rasjitiran kotun, Uwani Mustapha da kuma na daraktan watsa labaru, Festus Akande sun bayyana cewa a yanzu dai wannan magana jita jita ne kawai, sai dai wata majiya ta karkashin kasa dake kusa da Onnoghen ta tabbatar da murabus din nasa.

“Dama tun a ranar Alhamis muke sa ran zai mika wasikar yin murabus, don haka ba zamu yi mamaki ba idan har ya yi hakan a yau.” Inji majiyar dake kusa da dakataccen Alkalin Alkalan, Walter Onnoghen.

Sai dai daraktan watsa labaru na kotun koli, Akande ya tubure akan rashin sahihancin rahoton yin murabus da ake cewa Onnoghen yayi, inda yace idan har ya mika takardar ajiye aiki, lallai sai kotun koli ta sani, kuma shima zai sani.

Idan za’a tuna a ranar Larabar data gabata ne majalisar shari’a ta koli ta mika rahoton sakamakon binciken data gudanar akan bahallatsar Onnoghen ga shugaba Buhari, inda ta nemi a baiwa Onnoghen daman yin murabus tunda ta tabbata akwai guntun kashi a gindinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel