Tsaro: Malami ya bukaci Sarkin Musulmi ya kira taron addu'a na wata daya

Tsaro: Malami ya bukaci Sarkin Musulmi ya kira taron addu'a na wata daya

Dakta Bashir Yankuzu, babban limamin masallacin Jami'ar Fasaha ta MInna ya bukaci Sultan na Sokoto, Sa'ad Abubakar ya umurci musulmi su fara addu'ar 'Al-Qunut' a kullum domin rokon Allah ya kawo karshen garkuwa da mutane da sauran kallubalen tsaro da ake fama da shi a kasar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Dakta Yankuzu ya yi wannan kirar ne yayin wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai, NAN a garin Minna.

"Akwai lokacin da akayi garkuwa da wasu mutane a zamanin Manzon Allah (SAW) hakan yasa suka rika gudanar da wata addu'a ta musamman da ake kira 'Al-Qunut'.

Garkuwa da mutane: Malami ya bukaci Sarkin Musulmi ya kira taron addu'a na wata daya

Garkuwa da mutane: Malami ya bukaci Sarkin Musulmi ya kira taron addu'a na wata daya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kannywood: Nafisa Abdullahi ta soki Buhari a kan kashe-kashen Zamfara

"Ina bukatar shugabanin musulmi karkashin jagorancin Sultan na Sokoto, Sa'ad Abubakar su bayar da umurnin fara addu'a ta musamman domin kawo karshen satar mutane, satar shanu, fashi da makami da sauran barna da ake yi.

"Musamman yanzu da muka cikin watan Sha'aban saboda mu shiga watan Ramadan a cikin addu'o'i da kusanci ga Allah (SWT).

"Ina kyautata zaton Allah zai amsa addu'an mu wurin warware mana matsalolin tsaro da muke fama da shi a kasar nan.

"Kiristoci suma suna iya nasu addu'o'in na musamman domin duk tare muke fuskantar matsalolin kuma dukkan mu bayin Allah ne da ke amsa addu'an wadanda ake zalunta."

Ya ce yawaita addu'o'i ne zai taimakawa Najeriya wurin magance ta'addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin makiyaya da manoma da sauran matsalolin da ke adabar kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel