Da duminsa: 'Yan sanda sun kama mutane 2 bisa kisan da aka yiwa wani likita a Legas

Da duminsa: 'Yan sanda sun kama mutane 2 bisa kisan da aka yiwa wani likita a Legas

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ce an kama mutane biyu da ake zargi da hannu wurin kisar Stephen Urueye, Likitan da aka kashe a gaban asibitin koyarwa na Jami'ar Legas, LUTH.

Kakakin rundunar 'yan sanda, Elkana Bala ne ya tabbatar wa Sahara Reporters labarin a ranar Juma'a.

An kashe Urueye na a daren Alhamis a gaban kofar shiga LUTH da ke unguwar Idi-Araba a jihar Legas.

Daliban Jami'ar Legas sunyi zanga-zanga a kan kisar Urueye wanda ya hallarci taron yaye dalibai a Jami'ar ta Legas a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Kannywood: Nafisa Abdullahi ta soki Buhari a kan kashe-kashen Zamfara

Yanzu-yanzu: An kama mutum 2 da ake zargi da kashe likita kwana daya bayan kammala karatunsa

Yanzu-yanzu: An kama mutum 2 da ake zargi da kashe likita kwana daya bayan kammala karatunsa
Source: Twitter

Masu zanga-zangan sun ce hanyar Idi-Araba tayi kaurin suna a kan fashi da makami da kashe-kashe.

"Muna son rundunar 'yan sanda ta dauki mataki a kan lamarin," kamar yadda daya daga cikin masu zanga-zangan ya shaidawa majiyar Legit.ng

"Mu likitoci ne masu ceto rayukan al'umma. Bai dace mu rayukan mu su kasance cikin hatsari ba."

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce an kama mutane biyu kuma a halin yanzu ana yi musu tambayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel