Noma ya kamata matasa su fara kafin shiga siyasa – Ministan Gona

Noma ya kamata matasa su fara kafin shiga siyasa – Ministan Gona

Ministan noma da raya karkara, Audu Ogbe, ya shawarci matasa da su karfafa zuciyoyin su wajen fara harkar noma kafin su tunkari gaganiyar shiga siyasa.

Ogbe ya bayar da wannan shawara ce a jiya Alhamis, 4 ga watan Afrilu a Abuja, yayinda ya halarci wajen rattaba hannu a kan yarjejeniya tsakanin kamfanin NAMEL da kuma MANTRAC Nigeria Limited.

An dai kulla yarjejeniyar ne tsakanin kamfanonin biyu domin samar wa matasa filin noma har hekta 500,000 da za a yi amfani da ita,wajen bunkasa samar da abinci a kasar Najeriya.

Noma ya kamata matasa su fara kafin shiga siyasa – Ministan Gona

Noma ya kamata matasa su fara kafin shiga siyasa – Ministan Gona
Source: Depositphotos

Ogbe ya bayyana ta bakin daraktan ofishinsa, Victor Mayomi cewa ya kamata matasa su yi karatun ta-natsu, su fahimci cewa nauyin wadatar da kasar nan da abinci ya fa rataya ne a wuyan su, ba a wuyan kananan yara ko tsofaffi ba.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya fara tattaunawa da Goje

“Don haka ni ina jan hankalin ku da ku maida hankali a kan wannan gagarimin shirin noma domin sai da gudummar ku matasa sannan za a iya wadata kasar nan da abinci a nan gaba.

“Matasa su daina gagariniyar saurin shiga siyasa tukunna. Kamata ya yi su fi bada himma wajen shiga harkokin noma gadan-gadan. Idan suka wadata kasar nan da abinci, sai mu kara jin karfin damka musu amanar kasar nan.” Inji Minista Ogbe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel