Ku siyar da motana sannan ku cire N2m da ya rage a asusuna – Mutumin da aka sace a hanyar Kaduna-Abuja ya koka

Ku siyar da motana sannan ku cire N2m da ya rage a asusuna – Mutumin da aka sace a hanyar Kaduna-Abuja ya koka

Muntari Yusuf, wani ma’aikacin gwamnati da aka sace a hanyar Abuja zuwa Kaduna ya umurci iyalansa da su siyar da motarsa sannan su cire naira miliyan biyu da ya sauran masa a asusun bankinsa domin biyan kudin fansar da masu garkuwa dashi suka bukata.

An sace Yusuf tare da wasu matafiya da dama a ranar Talata da rana a hanyar babban titin yayinda suke tafiya zuwa Abuja.

A wani hiran waya da aka nada na Mallam Yusuf, da dan’uwansa Nura, da kuma daya daga cikin wadanda suka sace shi, da fari dai masu garkuwan sun bukaci naira miliyan 50.

A lokacin da iyalansa suka tara naira miliyan shida, sai masu karkuwan suka ki amincewa da hakan, inda suka bayyana lamarin a matsayin aikin banza.

Ku siyar da motana sannan ku cire N2m da ya rage a asusuna – Mutumin da aka sace a hanyar Kaduna-Abuja ya koka

Ku siyar da motana sannan ku cire N2m da ya rage a asusuna – Mutumin da aka sace a hanyar Kaduna-Abuja ya koka
Source: Facebook

Daga nan sai aka ji mallam Yusuf cikin murya mai rauni yana umurtan dan uwansa da ya ciro naira miliyan biyu daga asusunsa sannan ya siyar da motarsa domin a hada da sauran kudaden.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisar dattawa: Ndume ya fara tattaunawa da Goje

“Tunda kun yi nasarar hada naira miliyan shida, akwai muliyan biyu a asusuna. Kuna iya zuwa banki sannan ku cire. Idan kun cimma matsaya a tsakaninku, toh. Idan basu amince ba, ku siyar da mota na Toyota Rav 4.

“Na san halin da nake ciki. Don aka kada ku yi wa lamarin rikon sakainar kasha. Kada ku yi masu (masu garkuwa da mutanen) Magana mai zafi,” inji Yusuf.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel