Bayan kwanaki hudu da yankewa yar Najeriya haddi a Saudiya, an sake kama wani dan Najeriyan

Bayan kwanaki hudu da yankewa yar Najeriya haddi a Saudiya, an sake kama wani dan Najeriyan

Bayan kwanaki hudu kacal da tsayarwa wata yar Najeriya haddin kisan kai sakamakon safarar muggan kwayoyi, an sake kama wani dan Najeriya mai suna, Saheed Sobade, da Gram 1,183 na hodar Iblis a birnin Jiddah, kasar Saudiyya.

Babbar hadimar shugaban kasa kan harkokin wajen Najeriya, Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin hira a tashar Arise TV.

KU KARANTA: Ka tabbatar da Tanko Muhammad matsayin alkalin alkalai na din-din-sin - Majalisar Shari'a NJC ta bukaci Buhari

Tace: "Akwai wani labarin takaici da zan baku. Jiyan nan, ana cikin tunani kan yan Najeriya 20 da za'a tsayarwa haddi, bayan takwas da aka yankewa, an kama wani dan Najeriya da hodar Iblis."

"An kamashi da giram 1,183 na hodar Iblis. Ana kamashi aka sanar da ofishin jakadanci kuma sunarsa, Saheed Ayinde Sobade."

"Abin takaici ne ace a wannan zamani muna hada laifuka da kabilanci. Laifi laifi ne. Kada mu kayar da mutuncin katin fita kasar waje na Najeriya."

"Kada mu bari wasu yan tsirari su bata mu a idon duniya. Fashin Dubai ko ina an gani. Mun ga yadda aka bayyana hotunansu kuma babu wni dalili da zai hanamu bayyana hakan."

A kan matar da aka tsayarwa haddi a Saudiyya, mun sanar da iyalinta kafin bayyanawa duniya. Sunanta Kudirat Adesola Afolabi kuma tanada yara biyu."

A bangare guda, Majalisar koli ta bangaren shari'a NJC ta baiwa shugaban Muhammadu Buhari shawarar yiwa dakataccen alkalin alkalai, Walter Nkanu Onnoghen, ritayan dole.

Bayan tattaunawar da sukayi kan tuhumce-tuhumcen da hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC tayi masa, mambobin NJC sun zanna ranar Laraba kuma sun yi ittifakin cewa Walter Onnoghen bai cancanci cigaba da zama Alkali ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel