Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Buhari sun samu sabinin ra’ayi da APC

Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Buhari sun samu sabinin ra’ayi da APC

Kungiyar magoya bayan shugaba Buhari mai suna Buhari Youth Organisation (BYO) tare da hadin kan kungiyoyin matasa a yankin arewa ta tsakiya, sun bayyana rashin amincewarsu kan tsarin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta kawo, kan yanda zata raba ma yankuna mukaman majalisar dokokin kasar.

Mista Debit Joseph, jagoran kungiyar a yankin Arewa ta Tsakiya ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai day a gudana a Keffi, jihar Nassarawa, a ranar Juma’a, 5 ga watan Afrilu.

Joseph yace rashin amincewarsu ya kasance musamman akan tsarin kai ma yankin kudu shugabancin majalisan wakilai.

Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Buhari sun samu sabinin ra’ayi da APC

Shugabancin majalisa: Kungiyar matasan Buhari sun samu sabinin ra’ayi da APC
Source: UGC

A cewarsa, idan aka yi la’akari da gudumuwar kuri’u mai tarin yawa da yankin Arewa ta Tsakiya ta bayar, za a ga cewa yankin ta taka muhimmiyar rawar gani wajen tabbatar da nasarar APC a zaben da ya gabata, yankin ta cancaci fitar da kakakin majalisar wakilai.

KU KARANTA KUMA: Fafutukar neman shugabancin majalisa: Lawan ya gana da gwamnonin APC

Joseph har ila yau, ya roki shugabancin APC da su yi duba ga bukatar kungiyar sannan su sake duba wannan shiri na rabe-raben don tabbatar da cewa ba a bar masu ruwa da tsaki a baya ba.

Har ila yau, ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, zababbun gwamnonin APC, Sanatoci da yan majalisan wakilai murna, bisa nasara da suka samu a zaben da ya gabata.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel