Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

Hukumar EFCC ta tarawa Najeriya biliyan N251 a cikin watanni 16

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta tarawa Najeriya makudan kudade daga farkon watan Janairu shekarar 2018 zuwa wannan watan da mu ke ciki

- Sanarwar hakan ta fito daga bakin shugaban hukumar mai rikon kwarya, Ibrahim Magu

A jiya ne shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na rikon kwarya, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa hukumar ta samu damar ta kwace kudade wanda adadinsu ya kai kimanin biliyan N251 daga watan Janairun shekarar 2018 zuwa yanzu.

Shugaban ya bayyana hakan jiya Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, a lokacin da ya ke gabatar da kasafin kudin hukumar na shekarar 2019, ga kwamitin da ta ke da alhakin hakan, wanda dan majalisar wakilai na tarayya Kayode Oladele (APC, Ogun) ya ke jagoranta.

Ko kun san irin biliyoyin da EFCC ta tarawa Najeriya daga 2018 zuwa yanzu
Ko kun san irin biliyoyin da EFCC ta tarawa Najeriya daga 2018 zuwa yanzu
Source: Depositphotos

"Bayan kudi kuma akwai gwala-gwalai, kudade na kasashen waje da dai sauransu. Sauran bayani game da kudaden yana cikin takardun da muka gabatar muku," in ji shugaban hukumar.

"A farkon shekarar 2019, hukumar mu ta samu damar kwace kudi wanda adadin su ya kai biliyan N155," in ji Magu.

KU KARANTA: Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

Bayan haka kuma Magu ya bayyana kudurin hukumar na karawa ma'aikata 970 albashi da alawus.

A na shi bangaren kuma, shugaban kwamitin Oladele, ya bayyana cewa kwamitin za ta cigaba da iya bakin kokarinta domin ganin wannan gwamnatin ta yi nasarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel