Kasar Saudiyya ta kare kanta a kan kisan 'yar Najeriya

Kasar Saudiyya ta kare kanta a kan kisan 'yar Najeriya

Kasar Saudiyya ta ce an bi dukkan dokoki da hanyoyin shari'a kafin zartar da hukuncin kisa a kan 'yar Najeriya mai suna Mrs Kudirat Adesola Afolabi.

Saudiyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa ta ofishin jakadancin ta na Abuja ya fitar a matsayin martani bisa kalaman mai taimakawa shugaban kasa na musamman a kan harkokin kasashen waje, Mrs Abike Dabiri-Erewa da aka wallafa a jaridar The Nation.

Sanarwar ta kuma ce an zartar da hukuncin kisar ne bayan an gudanar da bincike mai zurfi kuma an tabbatar cewa laifin da ake tuhumanta da aikatawa ya tabbata.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Kasar Saudiyya ta kare kanta a kan kisan 'yar Najeriya

Kasar Saudiyya ta kare kanta a kan kisan 'yar Najeriya
Source: Twitter

"Ana bin dukkan dokoki da tsare-tsaren doka kafin zartar da hukuncin kisa a kasar Saudiyya kamar yadda shari'ar addinin musulunci ya tanada. Wannan shine abinda masarautar Saudiyya ke tafiya a kai," inji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ce an bawa dukkan wadanda ake zargi lauyoyi da za su kare su, kasar ta Saudiyya na samar da lauyoyi ga wadanda ba su da kudin daukan lauyan su.

Ma'aikatan kasashen waje ta Najeriya ta ce ofishin jakadancin Saudiyya ba ta tuntube su ba kafin zartar da hukuncin kisa a kan Mrs Afolabi sai dai an gayyaci su ne a ranar zartar da hukuncin a ranar 1 ga watan Afrilu.

Sai dai a bangarenta, ofishin jakadancin na Saudiyya ta musanta hakan inda ta ce ta kasance tana sanar da ofishin jakadancin Najeriya da ke Riyadh da Jeddah da sauran jami'an Najeriya na kasar duk halin da ake ciki.

Daga karshe sanarwar ta ce Saudiyya za ta cigaba da zartar da hukunci a kan dukkan wadanda aka samu da laifin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar domin kare 'yan kasar ta daga sharin kwayoyin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel